Wadansu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kashe manoma shida a Nasarawa
- ‘Yan kabilar Tibi na bukatar dauki daga gwamnatin tarayya da na jihar Nasarawa
- Wata mata a kauyen ta tabbatar da cewa Fulani ne suka kai harin
- Maharan sun bi dare ne suka harin da ya hallaka ‘yan kabilar Tibi
Kimannin manoma shida aka kashe a wani hari da wadanda ake zargin makiyaya ne suka kai a Karamar Hukumar Keana cikin Jihar Nasarawa.
Da yake tabbatar da kisan, Shugaban kungiyar al’ummar Tibi a Jihar Nasarawa, Kwamred Peter Ahemba ya ce kusan manoma shida ‘yan kabilar Tibi wadansu da ake zargin makiyaya suka kashe.
Ya ce maharan da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan kauyen Tse-Jimin, da ke masarautar Aloshi a Karamar Hukumar Keana da misalin karfe 9:45 na daren jiya.
Ya ambata sunayen wadanda aka kashen yayin harin: Batholomi Yahaya da Mnena Gideon da Ityokugh Yakubu da Timothy Aye da Ababi Tsavbee da kuma Blessing Oliver.
KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa
KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa
A cewar Shugaban, wata da ta tsallake rijiya da baya a harin ta tabbatar da cewa maharan Fulani ne makiyaya.
“Kira na ga gwamnatin Jihar Nasarawa shi ne ta tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar ciki har da al’ummar Tibi mazauna jihar. Wannan harin abin takaici ne, yace.
“Abin takaici ne matuka, kawai sun shigo suka kai wa mutanenmu hari. Don haka ina kira ga gwamnatin Jihar Nasarawa da na tarayya da su kawo wa al’ummar Tibi mazauna Jihar Nasarawa dauki.
“Ana neman a kawar da mu, suna korar mu daga Jihar Nasarawa ba mu san dalilin hakan ba."
Ya kara da cewa su mutane ne masu kaunar zaman lafiya, sun himmatu sosai wajen zaman lafiya da dukkanin kabilu mabanbanta da ke Jihar Nasarawa.
A bangare guda, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna baiwa mutane N5,000 zuwa N10,000 domin su zama masu kai musu bayanai ko kuma yi musu safarar makamai.
Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin jawabin ranar damokaradiyya da kuma bikin tunawa da ranar da ya hau karagar mulkin jihar Borno.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Zulum yace akwai bukatar shawo kan matsalar talauci a kasar nan inda ya jajanta yadda 'yan ta'addan cikin sauki suke jan mutane zuwa kungiyarsu.
Asali: Legit.ng