An kama sojan da aka kora daga aiki a cikin gungun ‘yan fashi, hoto

An kama sojan da aka kora daga aiki a cikin gungun ‘yan fashi, hoto

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen birnin tarayya, Abuja, ta yi bajakolin Friday Audu, korarren soja, tare da ragowar abokan sa16 bisa aikata laifukan fashi da makami, fyade da kuma damfara.

Da ya ke bajakolin ma su laifin a yu, Talata, kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, Bala Ciroma, y ace sun yi nasarar kma ma su laifin ne bayan aiki tukuru wajen gano maboyar ‘yan ta’adda a kwaryar garin Abuja da kewaye.

Y ace jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke wani mai suna Goodluck Onyewenyi, mai shekaru 40, saboda aikata laifin zamba ta hanyar bude asusun banki da sunan wani marar lafiya da ke neman taimakon kudi domin yi ma sa dashen koda.

An kama sojan da aka kora daga aiki a cikin gungun ‘yan fashi, hoto
An kama sojan da aka kora daga aiki a cikin gungun ‘yan fashi
Source: Twitter

Mai laifin na da kusanci da maras lafiyar, da wannan damar ya yi amfani wajen bude asusun banki tare da rubuta takardun neman taimakon kudi zuwa ma’aikatun gwamnati da manyan jami’an gwamnati,” a cewar kwamishin Ciroma.

DUBA WANNAN: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Kwamishinan ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke Friday Audu, korarren soja, bias laifin safarar bindigu ga gungun ‘yan fashi da makami da aka kama ranar 27 ga watan Disamba a yankin Nyanya.

Kazalika, kwamishinan ya ce sun kama wasu mutane uku – Ibrahim Iliya, Rilwanu Abdullahi da Victor Besini – a ranar 8 ga watan Janairu a Yangoli da ke Kwali da wani babban babur na musamman na sata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel