Hukumar Sojin Najeriya Ta Sallami Ibrahim Abdullahi, Kan Laifin Sata

Hukumar Sojin Najeriya Ta Sallami Ibrahim Abdullahi, Kan Laifin Sata

  • Hukumar Sojojin Najeriya ta kori wani kofur da aka kama da laifin sata da damfara a Benin
  • Hukumar ta yi kira ga daukacin al'umma su sani daga yau ba soja bane kuma kada a kulla harkalla da shi
  • Wannan shine karo na biyu cikin wata guda da hukumar za ta sallami wasu jami'anta bisa laifuka da ka iya kunyata hukumar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - Hukumar Sojin Najeriya ta sallami daya daga cikin jami'anta, Ibrahim Abdullahi, daga aikin aikin Soja bisa laifin sata, Jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

Ibrahim Abdullahi wanda Lance Kofur ne yana aiki a makarantar sufuri ta hukumar Soji Nigerian Army School of Supply and Transport (NASST), dake Ugbowo, Benin City, jihar Edo, gabanin sallamarsa.

An sallamesa ne ranar 8 ga Satumba, 2022 kan laifukan damfare-damfare da yawa.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

A jawabin sallamarsa, hukumar tace:

"An sallamesa yau 08/09/22 daga hukumar Sojin Najeriya kan laifin sata da damfare-damfare."
"An yanke masa hukunci ne a NASST Benin City, kada ku shiga wata harkalla da sallamammen Sojan."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

LCPL IB
Hukumar Sojin Najeriya Ta Sallami Ibrahim Abdullahi, Kan Laifin Sata Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

Rundunar Soji Ta Kori Sojoji Biyu Kan Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

A baya, hukumar Sojin Najeriya ta sallami Sojojinta guda biyu daga aiki kan kisan babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe.

Channels tv ta ruwaito cewa sojojin da korar ta shafa sun haɗa da, Lance Kofur John Gabriel da kuma Lance Kofur Adamu Gideon.

Muƙaddashin kwamandan Bataliya ta 241 da ke sansani a Nguru, jihar Yobe, Laftanar Kanal Ibrahim Osabo, ya shaida wa ƴan jarida cewa kwamitin binciken da aka kafa da haɗin kan yan sanda ya kama su da aikata laifin kisan.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi

Asali: Legit.ng

Online view pixel