Ganduje: An Sake Bankado Yadda Tsohon Gwamnan Ya Karkatar da N51.3bn, an Gano Dalili
- A sake bankado yadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya karkatar da N51.3bn wanda aka ware domin kananan hukumomi
- Shugaban hukumar yaki da cin hanci a Kano, Muhyi Magaji Rimingado shi ya tabbatar da haka yayin hira da manema labarai
- Hakan ya biyo bayan zargin tsohon gwamnan wanda kuma ke jagorantar jam'iyyar APC ta kasa da zargin badakalar kudi lokacin mulkinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugaban hukumar yaki da cin hanci a Kano, Muhyi Rimingado ya bayyana yadda suka zakulo wasu makudan kudi.
Muhyi ya ce hukumar ta gano N51.3bn wanda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya karkatar.
Yadda Ganduje ya karkatar da kudin
Shugaban hukumar ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce kudin na daga cikin N100bn da aka ware na kananan hukumomi, Cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An tura kudin ne zuwa kananan hukumomi kafin a hada baki da wasu ma'aikata inda aka karkatar da kudin."
"Mun samu kudin ne a asusun bankunan mutane daban-daban wanda suka tanadi wani a gidan gwamnati da ya ke ƙirga kudin da na'ura."
"Bayan haka sun sauya kudin daga naira zuwa dala tare da daukarsu zuwa wasu mutane, muna da ɗan canji da ya tabbatar da cewa an tura masa kudin kuma an sauya su zuwa dala."
- Muhyi Magaji
Sauran zarge-zarge kan Ganduje
Rimingado ya ce kusan mutane 200 sun tabbatar da yadda gwamnatin Ganduje ta tilasta su yin karya kan yadda aka kashe kudin a lokacin.
Ya kara da cewa Ganduje ya siyar da wani kamfani mallakin gwamnatin jihar kan farashin kudi abin takaici ga iyalansa.
Ya bayyana cewa sun tanadi gamsassun hujjoji da za su yi amfani da su domin shigar da kara, cewar Channels TV.
Ɗan Ganduje ya ziyarci Rimingado a Kano
A wani labarin, kun ji cewa ɗan shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara ofishin yaki da cin hanci na jihar Kano.
Abdul’aziz Ganduje ya kai ziyarar ce wurin shugaban hukumar, Magaji Rimingado domin nuna goyon bayansa kan binciken Ganduje da ake yi.
Hakan ya biyo bayan zargin tsohon gwamnan jihar da badakalar kadarorin gwamnatin jihar yayin mulkinsa.
Asali: Legit.ng