JAMB ta yi Barazanar Kama Iyaye Masu Daurewa Yaransa Gindi a jarrabawa

JAMB ta yi Barazanar Kama Iyaye Masu Daurewa Yaransa Gindi a jarrabawa

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta gargadi iyaye da su daina shawagi a cibiyoyin da yaransu ke zana jarrabawar
  • Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya yi zargin wasu daga iyayen da kai kawo a kusa da cibiyoyin domin yin katsalandan a tsarin tafiyar da jarrabawar
  • Hukumar ta yi barazanar cafke duk iyayen da aka kama suna shawagi a cibiyoyin jarrabawar ganin yadda suke karya dokar kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta yi barazanar kama duk iyayen yaran da aka gani suna shawagi lokacin da yaransu ke zana jarrabawar UTME.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Mai Magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin ne ya bayyana matsayar lokacin da yake ganawa ta yanar gizo da masu cibiyoyin gudanar da jarrabawar a Larabar nan.

Hukumar JAMB ta yi barazanar kama iyayen yaran da ke shawagi a cibiyoyin jarrabawa
JAMB ta ce bai kamata iyaye su dinga shawagi lokacin da yaransu ke rubuta jarrabawa ba: Jamb Official
Asali: Facebook

Fabian, ya ce wannan umarni ne na kai tsaye daga shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya jaddada cewa za a iya korar yaran duk iyayen da aka kama yana shawagi a kusa da cibiyoyin rubuta jarrabawar, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JAMB ta bayyana dalilin daukar matakin

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa daukar matakin ya zama dole ganin yadda wasu iyayen ke katsalandan cikin yadda yaransu ke gudanar da jarrabawar.

Haka kuma ya ce an samu wasu iyayen a baya da kawo matsala yayin gudanar da jarrabawar, da kuma shiga lamarin wadanda ke sa ido kan jarrabawar, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Farfesa Ishaq Oleyede ya ce;

“Hukumar na jaddada cewa tsare-tsaren ilimi na kasa ya tabbatar da cewa dole sai dalibi ya kai shekara 17 kafin ya rubuta jarrabawar.”
“Akwai shaidar wasu iyayen ba su bar yaransu sun kammala ajujuwan kamar yadda tsarin yake, saboda haka ne suke bin yaransu wurin gudanar da jarrabawar domin ganawa da masu kula da jarrabawa.”

An kama shugaban cibiyar rubuta JAMB

Jami’an rundunar yan sanda a jihar Kebbi sun bayyana cafke manajan wata cibiya JAMB da ke Zuru a karamar hukumar Zuru a jihar mai suna Abubakar Isma’il.

Ana zargin Abubakar Isma’il da laifin satar Kwamfutocin cibiyar kirar HP masu tarin yawa, kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora ya shaidawa manema labarai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel