Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 a Zamfara, Fusatattun Matasa Sun Yi Zanga-Zanga
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Tsafe da ke jihar Zamfara inda suka yi artabu da sojoji
- A yayin artabun ne aka ruwaito harsasai sun samu wasu fararen hula guda uku wadanda suka mutu nan taike yayin da wasu suka jikkata
- Rundunar 'yan sandan jihar wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana cewa jami'an tsaro sun dawo da zaman lafiya a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsafe, jihar Zamfara - Akalla fararen hula 3 ne suka mutu yayin da wasu uku suka samu raunuka a yayin wata arangama tsakanin dakarun Operation Hadarin Daji da ‘yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa harsashi ne ya kuskure ya samu fararen hular a yayin artabun a kauyen Tsafe da ke jihar Zamfara, a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu.
Yan bindiga sun farmaki kasuwa
Zagazola Makama ya ruwaito cewa, ‘yan fashin na sanye ne da kayan mata, yayin da wasu kuma suka sanya kayan jami'an tsaro kafin su kai hare-haren a wurare daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar leken asirin ta shaida wa Makama cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wata mota da ke jigilar ‘yan kasuwa zuwa garin Tsafe ta hanyar Gusau zuwa Tsafe.
Haka kuma wasu ayarin 'yan bindigar a kan babura sun shiga kasuwar kauyen tare da bude wuta kan mai uwa da wabi bayan sun bi ta ofishin 'yan sanda na garin.
Rundunar 'yan sanda ta magantu
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar wa da gidan talabijin na Channels kai harin ta wayar tarho.
Ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda harin ya rutsa da su ba amma ya ce an tura jami’an hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda zuwa wurin domin fatattakar ‘yan ta’addan.
"Har yanzu ina jiran DPO na Tsafe ya ba da cikakken rahoton halin da ake ciki amma abin da zan iya tabbatar muku a yanzu shi ne sojoji da ‘yan sanda sun awo da zaman lafiya yanzu.”
- A cewar Abubakar.
Matasa sun yi zanga-zanga a Tsafe
A hannu daya kuma, Zagola Makama ya ba da rahoton cewa jami’an tsaro sun tarwatsa wasu fusatattun matasa bayan da suka yi zanga-zangar nuna adawa da jami’in ‘yan sandan Tsafe.
Mazauna yankin sun fusata ne saboda jami’an ‘yan sandan ba su yi wani yunkuri na dakile ‘yan bindigar ba a yayin da suka far wa mazauna yankin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta aike da wata tankar yaki mai daukar jami'ai zuwa tsafe domin dakile masu zanga-zangar.
Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa akalla mutane 13 suka mutu yayin da sama da 40 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Kadua.
Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya reshen jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da alakanta shi da gudun sa a da kuma yin lodin da ya wuce ka'ida.
Asali: Legit.ng