Mutum 13 Sun Mutu, Wasu 40 Sun Jikkata a Wani Mummuna Hatsarin Mota a Jihar Kaduna

Mutum 13 Sun Mutu, Wasu 40 Sun Jikkata a Wani Mummuna Hatsarin Mota a Jihar Kaduna

  • Hukumar FRSC ta ce wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Kaduna ya lakume rayuka 13 tare da jikkata wasu 40
  • Kwamandan FRSC reshen jihar, Kabir Nadabo, ya ce mutane 60 ne hatsarin ya rutsa da su bayan motar daukar albasa ta kwace
  • A Ogun, FRSC ta ce akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu tara suka samu raunuka a hadarurrukan da suka faru a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Akalla mutane 13 suka mutu, wasu 40 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ranar Juma’a a kan titin Ahmadu Bello, a cikin birnin Kaduna.

Kara karanta wannan

Yayin da ake zarginsa da sulalewa da Yahaya Bello, Gwamna ya roki Tinubu alfarma

Hukumar FRSC ta magantu kan hadarin da ya afku a Kaduna da Ogun
Hatsarin na jihar Kaduna ya afku ne a ranar Juma'a a kan titin Ahmadu Bello. Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare inda wata motar tirela da ke jigilar fasinjoji da albasa daga Kano ta kwace tare da afkawa kan wata motar da ke tafiya.

Mutane 60 hatsarin ya rutsa da su

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, Kabir Nadabo, ya dora alhakin hatsarin kan gudun wuce sa a da kuma yin lodi da ya wuce ka'ida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Nadabo, wanda ya shiga aikin aikin ceto wadanda hatsarin ya shafa ya ce mutane 60 ne iftila'in ya rutsa da su, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Barau Dikko da ke a birnin jihar.

Mista Nadabo ya ce direban tirelar ya gudu bayan hadarin amma ana kokarin gano shi da ma asalin mai motar.

Kara karanta wannan

'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya halaka bayin Allah sama da 10 a Arewacin Najeriya

Mummuna hatsari a jihar Ogun

A Ogun, akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu tara suka samu raunuka a wasu hadarurrukan da suka faru tsakanin Juma’a da Asabar.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda mutane biyu suka mutu yayin da daya kuma ya samu rauni Iyana Odogo kan hanyar Ilaro-Owode.

Mai magana da yawun hukumar FRSC a jihar Ogun, Florence Okpe ta bayyana cewa lamarin ya rutsa da wata mota kirar Mitsubishi da wata babbar mota.

Hatsarin mota: Mutane 25 sun mutu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa akalla mutane 25 suka mutu a wani mummunan hatsari da ya afku a jihar Kwara baya motoci uku sun yi karo da juna.

Yayin da mutane 15 suka samu raunuka, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta ce gudun wuce sa'a ne silar faruwar hatsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel