An Karbo Bashin Kaso 45% Na Kaduna Tun Kafin El-Rufai Ya Hau Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

An Karbo Bashin Kaso 45% Na Kaduna Tun Kafin El-Rufai Ya Hau Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

  • An gano gaskiya kan rade-radin cewa an ciyo bashin kaso 45% daga bashin da ake magana tun kafin Nasir El-Rufai ya hau mulki
  • Wani mai amfani da shafin X, Imran Wakili shi ya wallafa cewa tun kafin El-Rufai ya karbi mulki a 2015 aka ciyo bashin fiye da kaso 45%
  • Sai dai binciken kwa-kwaf da aka gudanar ya tabbatar da cewa El-Rufai ya ci bashin fiye da kaso 80% a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan tulin bashi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya tara, an gano gaskiya kan wata wallafa a shafin X.

Bayan Gwamna Uba Sani ya zargi El-Rufai da tara tulin bashi, wani mai amfani da kafar X, Imran Wakili ya ƙaryata abin da ake fada kan El-Rufai.

Kara karanta wannan

"Mulki babu tabbas": Aisha Yesufu ta tsokani El-Rufai da Yahaya Bello kan halin da suke ciki

An bankado gaskiya kan zargin El-Rufai ya samu bashin kaso 45% kafin hawa mulki
Gaskiya ta bayyana kan bashin da Nasir El-Rufai ya ci a Kaduna. Hoto: @ubasanius, @elrufai.
Asali: Twitter

Zargin El-Rufai ya samu bashin kaso 45%

Wakili ya wallafa a shafin X cewa kaso 45% na bashin an karbe su ne tun kafin El-Rufai ya hau mulkin jihar a 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zuwa ga Uba Sani da abokansa, farko dai ku sani bashin da ake magana kaso 45% daga ciki ba gwamatin El-Rufai ba ne ta ciyo kamar yadda kuke fada."
"Na biyu, gwamnatinka ba ta da tsari na kirkirar ko samar da arziki a jihar, idan ka bi tsarin El-Rufai Kaduna za ta iya samar da N10bn a kowane wata."
"Amma gwamnatinka ta fi kulawa da siyasa da kuma burge 'yan siyasa shiyasa ba za ka yi komai ba."

- Imran Wakili

Binciken da aka yi kan bashin El-Rufai

Sai dai Daily Trust ta bankado yadda lamarin ya ke tare da gano gaskiya kan wannan ikirari na Wakili.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jam'iyyar APC na shirin dakatar da Nasir El-Rufai? Gaskiya ta bayyana

Rahoton Hukumar kula da bashi a Najeriya, DMO ya tabbatar da bashin Kaduna kan N16bn a 2014 kafin El-Rufai ya hau mulki inda ya karu zuwa N87bn a 2023.

Bashin kasashen ketare ya na $234m a 2014 inda ya karu zuwa $569m a watan Yunin 2023.

Hakan ya tabbatar da cewa Nasiru El-Rufai ya ci bashin N70.5bn wanda ke nuna ya ci bashin kaso 80% na bashin jihar Kaduna.

Majalisa ta kafa kwamitin binciken El-Rufai

Kun ji cewa Majalisar jihar Kaduna ta kafa kwamiti domin binciken bashin da Nasir El-Rufai ya ciyo a jihar.

Hakan ya biyo bayan korafin Gwamna Uba Sani kan yawan bashi da mai gidansa ya bari a jihar da ke kawo wa gwamnatin cikas a harkokinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel