Taron NEC: Babban Jigo Ya Buƙaci Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Yi Murabus Nan Take

Taron NEC: Babban Jigo Ya Buƙaci Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Yi Murabus Nan Take

  • Duk da ya tsallake a taron kwamitin zartaswa NEC, muƙaddashin shugaban PDP ya ci gaba da fuskantar matsin lamba ya yi murabus
  • Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo, ya buƙaci Umar Damagum ya yi murabus matukar yana kishin PDP a zuciyarsa
  • Ya kuma yabawa taron NEC da aka gudanar ranar Alhamis, inda ya kara da cewa PDP za ta ci gaba da ƙara ƙarfi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jigo a People’s Democratic Party (PDP), Dakta Farah Dagogo ya bukaci mukaddashin shugaban jam’iyyar, Umar Damagum ya yi murabus daga mukaminsa.

Dogogo, tsohon ɗan majalisar tarayya daga jihar Ribas, ya roƙi Damagum ya yi murabus ne domin ya nuna kishin PDP, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Umar Damagum.
An nemi muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum ya yi murabus Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Ya kuma ayyana cewa taron kwamitin zartaswa (NEC) karo na 98 da PDP ta gudanar ranar Alhamis ya nuna karfin da take da shi wajen shawo kan matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi taron NEC

Idan baku manta ba gabanin taron NEC, an yi raɗe-raɗin cewa PDP ta kama hanyar faɗawa cikin wasu sabbin rigingimun cikin gida.

Hakan ka iya faru ne saboda yadda jam'iyyar ta fara tunanin bai wa Arewa ta Tsakiya damar maye gurbin kujerar shugaban PDP domin ƙarisa wa'adin Iyorchia Ayu.

Sai dai kuma Damagum ya samu nasarar ci gaba da jan ragamar jam'iyyar PDP daga nan har zuwa taron NEC na gaba wanda za a yi a watan Augusta.

Jigo ya buƙaci Damagum ya sauka

Da yake martani kan wannan matakin, Dokta Farah Dagogo ya ce wadanda ke da kishin jam’iyyar a zuciya za su sadaukar da komai a kan lokaci domin PDP ta tsaya da ƙafarta.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

Ya jaddada kwarin guiwarsa cewa ɗage taron NEC zuwa watan Augusta, zai ba Damagum damar gano cewa abin da ya fi kamata shi ne ya yi murabus.

"A ganina taron NEC ya samu nasara. Ba tare da wata tangarda ba, jam’iyyar PDP ta kammala taron ba tare da wata matsala ba kuma haka muke fata ta ci gaba da kara karfi.
"Eh, mukaddashin shugaban jam'iyya zai ci gaba da riƙe muƙaminsa, amma ya gani a zahiri cewa lokaci ya yi da zai bar muƙamin domin kafa shugabanci mai ma'ana a watan Augusta."

- Farah Dagogo.

Atiku ya mayar da martani

A wani rahoton kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya jaddada cewa babu wani mahaluƙi daga cikin ƴan Adam da ke bayar da mulki sai dai Allah maɗaukakin Sarki.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya faɗi haka ne yayin da wasu magoya bayansa suka fara zargin mambobin PDP sun ci amanarsa a taron NEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel