Yanzun Nan: Wasu 'Yan NNPP Sun Dakatar da Gwamnan Kano, Abba Na Watanni 6

Yanzun Nan: Wasu 'Yan NNPP Sun Dakatar da Gwamnan Kano, Abba Na Watanni 6

  • Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bisa amincewar wani tsagi na mahukunta ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • NNPP ta dakatar da Yusuf ne biyo bayan gayyatar da kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar ya yi masa kan zargin ayyukan zagon kasa
  • An ruwaito cewa gwamnan bai amsa wannan gayyatar ba, lamarin da ya sa jam'iyyar ta dakatar da shi na tsawon watanni shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin amintattu na wani bangare na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf.

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano
NNPP ta zargi Gwamna Yusuf da aikata ayyukan da suka sabawa jam'iyyar. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

An dakatar da Yusuf na tsawon watanni shida bisa zarginsa da hannu a cikin ayyukan da suka saba wa jam’iyyar, kamar yadda jaridar The Independent ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku vs Wike: An yi hasashen abin da zai faru a wajen taron NEC na PDP

Sakataren jam’iyyar na kasa na bangaren, Kwamared Oginni Olaposi Sunday, ya bayyana hakan a ranar Talata, a hedikwatarta da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi ake zargin Abba ya aikata?

Oginni ya ce dakatar da gwamnan ya biyo bayan gayyatar da aka yi masa ne na ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa kan abin da ya shafi kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Jaridar The Punch ta rahoto tsagin jam’iyyar ya ce ana zargin Gwamna Yusuf da laifin halartar taron kasa na wani bangare da kungiyar Kwankwasiyya ta shirya a Class Event Centre da ke Wuse.

Ya ce zuwan gwamnan wannan taro alhalin yana sane da cewa ya zama gwamna ne karkashin NNPP ya saba da kundin tsarin jam'iyya kuma aikin zagon kasa ne.

Matsayar NNPP kan Gwamna Abba

“Ya zama wajibi ‘yan Najeriya su san matsayin jam’iyyar New Nigeria People’s Party sakamakon gazawar da gwamnan ya yi a na gurfana gaban kwamitin ladabtarwar.

Kara karanta wannan

Mambobin NNPP sun buƙaci Gwamna Yusuf na Kano ya yi murabus cikin sa'o'i 48, ta faɗi dalili

“Tare da amincewar kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP da kuma shawarar bai-daya na kwamitin ayyuka NWC, muna sanar da dakatar da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano daga jam'iyyar na tsawon watanni shida."

- A cewar Oginni

Jaridar SaharaReporters ta rahoto Oginni ya ce jam'iyyar ta bai wa gwamnan duk wata dama da zai iya kare kansa game da zarge-zargen ayyukan zagon kasa amma yaki amsa gayyatar kwamitin.

Majalisar Kaduna za ta binciki El-Rufai

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kwamiti da zai binciki yadda Malam Nasir El-Rufai ya tafiyar da mulkin jihar.

Kwamitin zai kuma yi duba kan kudaden bashi da gwamnatin El-Rufai ta karbo, kudaden tallafi, da yadda tsohon gwamnan ya gudanar da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel