Najeriya Za Ta Fara Ƙera Motoci Gadan Gadan, Ministar Tinubu Ta Yi Bayani

Najeriya Za Ta Fara Ƙera Motoci Gadan Gadan, Ministar Tinubu Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin cewa yanzu Najeriya na da karfi da kayan aikin kera motoci, domin amfanin gida da kai wa waje
  • Ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite, ta tabbatar da hakan tana mai cewa komai zai kankama zuwa Disamba
  • Dr Uzoka-Anite ta ce idan har kasar ta gaza fitar da ababen hawanta zuwa karshen shekara, to a kama kamfanonin kerawar da laifin gazawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite, ta tabbatar da cewa a yanzu Najeriya na da karfi da kayan aikin kera motoci.

Gwamnati ta yi magana kan fara kera motoci daga watan Disamba
Dr. Doris Uzoka-Anite ta ce Najeriya na da karfi da kayan aikin kera motoci yanzu. Hoto: @DrDorisAnite
Asali: Twitter

La'akari da kyakkyawan yanayin aiki da gwamnati ke samarwa, ta ce za a dora alhaki kan kamfanoni idan ba a fara fitar da motocin ba daga watan Disamba 2024.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

A halin yanzu dai Najeriya na samar da kasa da kashi 10 na motocin da ake amfani da su a kasar, kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harkar kera motoci ta samu koma baya?

Rahotanni sun bayyana an cewa kiyasta kudin masana’antar kera ababen hawa a Najeriya ya kai kusan Naira biliyan 302.

Amma masana'antar ta samu koma baya a shekarar da ta gabata sakamakon hauhawar farashin kayayyakin kere-kere da kuma karancin bukatu na motoci na gida.

A cewar kididdigar shugabannin kamfanonin kere-kere (MCCI), kera motoci da hada su a Najeriya sun tabarbare zuwa kasa da maki 50 daga maki 48.6 zuwa 46.7, talabijin na Arise ya ruwaito.

Amma da take magana a taron masu kera motoci a Abuja, ministar ta bayyana cewa sana’ar kera motoci na fuskantar kalubale da kuma damarmaki a tare.

Kara karanta wannan

Ana tsoron Israila ta kai hari a Iran, an ji fashe fashe a inda aka tanadi nukiliya

"Za a kera motoci zuwa Disamba" - Aite

Sanarwar da daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Adebayo Thomas ya fitar ranar Juma’a, ta ce:

“Game da matsayar gwamnatin tarayya, muna ganin yanzu masana’antar kera motoci ta Najeriya ta shirya ta fara aiki gadan-gadan.
“A yanzu mun dora yakininmu akan dukkanin masu ruwa da tsaki domin ganin hakan ta tabbata. Idan ba mu fara fitar da motocin da aka kera a Najeriya ba kafin karshen wannan shekara (Decemba), to laifin ku ne."

Anite ta jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin kamfanoni, dillalai, hukumomin gudanarwa, da sauran masu ruwa da tsaki a masana'antar kera motoci.

Gwamnati ta fara ba da tallafin N50,000

A wani labarin kuma, ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite ta sanar da fara ba 'yan Najeriya tallafin N50,000 na yin sana'a.

Anite ta ce wannan na daga cikin shirin bayar da lamuni marar ruwa da yawa da shugaban kasa ya kaddamar domin tallafawa kananun 'yan kasuwa da masu sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.