Kamfanin Najeriya zai fara kera motoci masu anfani da iskar gas
Wani kamfanin kere-kere a Najeriya mai suna Power Gas ya shiga yarjejeniyar kasuwanci tare da kulla alaka da takwaran sa na kasar Austria domin fara kera motocin da ke anfani da iskar gas ba man fetur ba a Najeriya.
Kamar dai yadda kamfanin ya bayyana shirin na su zai fara karkata ne ga sauya fasali tare da samfurin motocin hayar da ake anfani da su a garuwan Legas da ma wasu dake a shiyyar kudu-maso-kudancin kasar.
KU KARANTA: Obasanjo ya kara caccakar Buhari
Legit.ng ta samu cewa kamfanin haka zalika ya bayyana cewa idan har hakan ta tabbata, to tabbas kasar za ta ci ribar kimanin dalar Amurka biliyan 2.5 duk shekara sakamakon rage anfani da man fetur din da hakan zai haifar.
A wani labarin kuma, Hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gwamnatin tarayya watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC a turance ta damke wani dan kasar Sin watau China mai suna Li Yanping da makudan kudaden da suka kai Dalar Amurka dubu 300 yana kokarin arcewa da su ya bar kasar.
Sai dai kamar yadda muka samu tuni har hukumar ta EFCC ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotu dake zaman ta a garin Legas inda aka tuhume shi da laifin yin safarar haramtattun kudaden kasar waje.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng