Jelani Aliyu ya ziyarci wurin kera sassan karfe na motoci Abuja
Shugaban hukumar nan dake ke kula da fasahar kere-kere da zanen taswirar ababen hawa ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau National Automotive Design and Development Council (NADDC) a turance watau Jelani Aliyu ya kai wata muhimmiyar ziyara.
Shugaban dai ya kai ziyarar ne yau Alhamis 17 ga watan Janairun shekara ta 2018 zuwa ga wani babban kamfanin kera sassan karfe na motoci mai suna Gorgeous Metal Industries Limited dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Legit.ng dai ta samu cewa kamfanin da ya kaiwa ziyarar aiki ya shahara sannan kuma ya kware wajen kerwa tare da hada sassan motoci irin su tankoki da kuma bodi na manyan motoci.
A yayin ziyarar ta sa ya samu rakiyar babban darakta na ma'aikatar mai kula da sashen kamfunna da kere-kere mai suna Injiniya Waheed Kolapo.
A wani labarin kuma, Wata mata da ake kira da suna Jessica Cox da aka haifa ba tare da hannuwa ba a jihar Arizona, kasar Amurka ta jefa dukkan duniya cikin al'ajabi bayan da ta kammala karatun ta na tukin jirgin sama.
Matar mai shekaru 35 a duniya dai majiyar mu ta samu cewa itace mace ta farko da ta taba samun wannan horon a duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng