Jirgin Sojoji Ya Kuma 'Kashe' Mutane Ana Shirin Sallar Idi a Kauyen Zamfara
- Ana zargin sojoji sun yi kuskure sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula a yunkurin kashe ‘yan bindiga a Zamfara
- Mutanen kauyen Muradun sun tabbatar da cewa bam ya hallaka bayin Allah sama da 30 ana shirye-shiryen sallah
- Sojoji sun kafe cewa sai da suka yi binciken da ya kamata kafin su saki wuta, mazauna yankin suna da ja a kan hakan
Zamfara - Wani luguden wuta da dakarun sojojin Najeriya suka yi ya hallaka mutane da-dama a wani kauye da yake a jihar Zamfara.
Akalla mutane 33 suka mutu a sakamakon wannan hari kamar yadda wani mai sarautar gargajiya da wasu mazauna suka shaida.
Muradun: Sojoji da kuskuren kashe mutane
Reuters ta rahoto cewa sojoji sun hallaka bayin Allah yayin da suke kokarin fatattakar masu garkuwa da mutane a mabuyarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan lamari da ya faru a ranar 10 ga watan Afrilun 2024 yana zuwa ne bayan a baya sojojin sama sun yi ta kuskuren kashe mutane.
Sojoji sun tabbatar da barin wuta da suka yi ta sama ya hallaka ‘yan bindiga da-dama a karamar hukumar Muradun a jihar Zamfara.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga ko farar-hula?
Amma Mai martaba Lawali Ango wanda shi ne Hakimin Dogon Daji ya shaidawa gidan jaridar cewa babu ‘yan bindiga a kasarsa.
Alhaji Lawali Ango ya ce mutane suna shirin zuwa masallacin idi a kauyensa sai suka hangi jirgin sama, can sai aka ji wani kara.
Ana zargin sojoji sun kashe mutane 33
Da zuwan mutane inda abin ya faru, basaraken ya ce an iske bam ya kashe yara, mata da maza a wani gda, an rasa mutum 33.
Basaraken ya ce sojojin kasar suna ikirarin ‘yan bindiga sun fake a kauyensu, amma ya kalubalanci batun, ya ce sam ba haka ba ne.
Sojoji sun kashe masa mata da yara?
The Cable ta bibiyi rahoton, ta ce wani Surajo Abubakar wanda manomi ne a kauyen ya rasa matansa biyu da ‘ya ‘ya biyar a harin.
Wani mutum ya ce ya ga wadanda aka kashe, kuma sun iya hada gawawwakin sun yi masu sallar jana’iza, sannan aka birne su.
Wasu da aka zanta da su sun tabbatar da mutuwar fararen hula a Muradun, sai dai sojojin sun ce ba a kashe wasu fararen hula ba.
Sojoji sun kashe mutane a Tudun Biri
Hakan ta faru a shekarar bara da masu bikin maulidi a garin Tudun Biri da ke Kaduna, hakan ya jawowa sojojin sama suka sosai.
Idan za a tuna, wani Bawan Allah da ke zaune a kauyen Tudun Biri ya ce duka ‘ya ‘yansa shida sun rasu da aka jefo masu bam ranar.
Asali: Legit.ng