DHQ: Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga Sama da 150, Sun Samu Nasarori a Arewacin Najeriya

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga Sama da 150, Sun Samu Nasarori a Arewacin Najeriya

  • Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan bindiga 188 tare da kama wasu 330 a cikin makon da ya gabata a Arewacin ƙasar nan
  • Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce ga dukkan alamu sojoji sun kamo hanyar kawo ƙarshen duk wani nau'in ta'addanci
  • Buba ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato makamai masu ɗumbin yawa tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe akalla ƴan ta'adda 188 a ayyukan da suka gudanar a Arewacin ƙasar nan cikin mako ɗaya da ya shuɗe.

Bayan haka dakarun sojojin sun cafke wasu ƴan bindiga 330 tare da kubutar da mutane 133 daga hannun masu garkuwa da su a tsawon wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Okuama: Sojoji sun kai samame wani kauye, sun kama shugaban al'umma da wasu mutum 10

Sojojin Najeriya.
Sojojin sun samu manyan nasarori kan ƴan ta'adda a makon jiya Hoto: Defence HQ Nigeria
Asali: Getty Images

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Edward Buba ya kara da cewa nasarorin da sojojin suka samu a baya-bayan nan ya nuna yadda suke da karfi da shirin kakkaɓe ayyukan ta'adanci a faɗin ƙasar nan.

Sojojin sun shirya tsare mutane

"Sojoji suna aiki tukuru domin murƙushe ‘yan ta’adda, dakile rashin tsaro, da kuma tsare rayukan ‘yan kasa. Saboda haka ƴan ta'adda na ɗanɗana kuɗarsu fiye da wahalar da suke jefa mu a ciki.
"A cikin makon da ake magana a kansa, sojoji sun kashe ƴan bindiga 188 tare da kama wasu 330. Sannan sun kuma ceto mutane 133 da aka yi garkuwa da su.
"A halin yanzu sojoji sun kai mataki mai ƙarfi a yaƙin da suke da ƴan ta'adda, sun kashe manyan ƴan bindiga. Zamu ci gaba da kokarin samar da tsaro ga ƴan Najeriya."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun dira sansanin manyan ƴan bindiga 3 a Arewa, sun kashe da yawa ranar Sallah

- Manjo Janar Edward Buba

An kwato manyan makamai

Kakakin DHQ ya ce dakarun sojojin sun kwato makamai kala daban-daban 270 da alburusai iri-iri 5,083, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Legit Hausa rahoton cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa Maris din shekarar 2024, sojojin sun kashe jimillar 'yan ta'adda 2,351 tare da kama 2,308.

Haka nan kuma, dakarun sojojin sun kubutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su a tsawon waɗannan watanni.

Sojoji sun kashe tulin ƴan bindiga

A wani rahoton na daban Dakarun sojojin saman Najeriya sun farmaki sansanonin manyan ƴan ta'adda a kananan hukumomi 3 na jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama, Edward Gabkwet ya ce luguden wutan da jirage suka yi, ya halaka ƴan bindiga masu yawa ranar Sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel