Kasuwanci: Kasuwannin arewa 3 da suka fi tara da jama'a da hada-hadar cinikayya
Duka inda kasuwa take a duniya, wuri ne na tara jama'a da kuma gudanar da hada-hada da harkalla kala daba-daban. Babban amfanin kasuwa shine gudanar da saye da sayar wa. Ana sayar da abubuwa da dama a kasuwa daya, amma akwai wasu kasuwanni da aka ware domin sayar da wasu kayan amfani ko na masarufi.
Wani rahoto da aka wallafa ya bayyana sakamakon wani bincike da aka gudanar a kan manyan kasuwannin kasar nan da suka fi tara jama'a da kuma gudanar da hada-hadar kasuwanci. Mun zakulo wasu uku daga cikin wadannan kasuwanni da ke arewacin Najeriya.
1. Kasuwar Kurmi, Kano
Kasuwar Kurmi da ke jihar Kano na daya daga cikin tsofi kuma manyan kasuwannin Najeriya da ake hada-hadar kasuwanci. Tsohuwar kasuwa ce da aka kafa tun lokacin sarkin Kano Mohammed Rumfa a shekarar 1463.
Kasuwar ta fi shahara wajen sayar da kayan tarihi da na zamani da suka hada da kayan saki, jima, rini, kananan duwatsun kwalliya, kayan kwalliyar mata da kayan mata na saki (saka) da sauran su. Kazalika, ana sayar da kayan abinci da dabbobi da ragowar wasu abubuwa na bukatar jama'a.
DUBA WANNAN: NDLEA ta fadi jihar arewa da ta doke Kano a yawan masu safarar miyagun kwayoyi
2. Kasuwar Taminus, Jos
Bayan hada-hadar harkokin kasuwanci, kasuwar Taminus (Terminal Market) da ke garin Jos a jihar Filato ta kasance wurin ziyara ga bakin haure. An bayyana ta a matsayin babbar ginanniyar kasuwar zamani da babu irinta a fadin kasashen Afrika ta yamma. Ana hada-hadar kusan dukkan kayan amfanin gida da jama'a a kasuwar.
3. Kasuwar Doya ta garin Zaki Biam, Benue
Kamare yadda sunanta ya bayyana, hada-hadar Doya kawai ake yi a wannan kasuwa, kuma ita ce kasuwar Doya mafi girma a kasashen Afrika ta yamma. Kasuwa na yankin Sankera na karamar hukumar Ukum a jihar Benuwe. Ana noma zanganniyar Doya fiye da miliyan 1.5 a jihar Benuwe, lamarin da ya saka kasuwar ta zama a sahun gaba wajen cinikin Doya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng