Remi Tinubu: Matar Shugaban Kasa Ta Kaddamar da Shirin Tallafawa Matan Arewa

Remi Tinubu: Matar Shugaban Kasa Ta Kaddamar da Shirin Tallafawa Matan Arewa

  • Matar shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta kaddamar da shirin bada tallafi wa mata a jihar Borno
  • Uwargidar Najeriyar ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, yayin kaddamar da shirin
  • Ana sa ran shirin zai taimaka wajen bunkasa harkar noma tare da samar da ayyukan yi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Matar shugaban kasar Najeriya, Sanata Remi Tinubu ta kaddamar da shirin tallafawa mata da masu bukata ta musamman a jihar Borno.

Shirin ya gudana ne ranar Talata, 16 ga Afrilu a birnin Maiduguri, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu ta kaddamar da shirin noma ga matan Arewa

Remi Tinubu
Mata da masu bukata ta musamman ne za su mori shirin daga Arewa maso gabas. Hoto: Excellecy Remi Tinubu
Asali: Facebook

Dalilin bada tallafin Remi Tinubu

Bayanan da uwar gidar gwamnan jihar Gombe, Hajiya Asma'u Inuwa Yahaya, ta wallafa a shafinta na Facebook, ya nuna cewa an yi shirin ne domin ba mata tallafi a harkokin noma da kiwo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran shirin zai karfafawa mata gwiwa a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Taron wanda ya shafi rayuwar mata da dama da ke sana’ar noma da sauran kungiyoyin masu bukata ta musamman ya samu halartar uwargidar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima.

Matar mataimakin shugaban kasar ce ta wakilci uwargidan shugaban kasar Najeriya yayin kaddamar da tallafin.

Adadin wadanda suka samu tallafin

Shirin ya bada tallafi wa mata guda 120 tare da masu bukata ta musamman 200 a yankin Arewa maso gabas.

Kowacce mata daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin ta samu N200,000 yayin da kowanne mai bukata ta musamman ya samu N100,000.

Kara karanta wannan

Yayin da NEF ta yi da-na-sanin zaben Tinubu, shugabannin Fulani sun fadi matsayarsu

Remi Tinubu ta kaddamar da tallafin noma

Haka zalika kun ji cewa mai dakin shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu, ta kaddamar da shirin noma na gwamnatin tarayya ga mata a Arewa ta tsakiya.

Sanata Remi Tinubu ta bayyana cewa gwamnati na sane da muhimmancin manoma mata wajen ciyar da kasar nan gaba. Kuma an rarraba Naira miliyan goma ga kowace jiha domin bata damar tallafawa matan su yi nomansu da gaske

Asali: Legit.ng

Online view pixel