Gwamna Ya Sanya Dokar Ta Baci da Umarnin Harbe 'Yan Daba a Arewacin Najeriya

Gwamna Ya Sanya Dokar Ta Baci da Umarnin Harbe 'Yan Daba a Arewacin Najeriya

  • Gwamnatin jihar Niger karkashin jagorancin gwamna Umar Bago ta tabbatar da kafa dokar ta ɓaci a fadin jihar tare da bada izinin harbe 'yan daba nan take
  • Kafa dokar ya biyo bayan harin da wasu 'yan daba suka kai ne a unguwar Maitumbi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu
  • Hukumar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar harin tare da sanar da nasarar kama mutane shida da suka kai harin.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Umar Bango, ya kafa dokar ta-baci a jihar, bayan da aka kashe mutane biyu a wani hari da wasu ‘yan daba suka kai a unguwar Maitumbi da ke Minna, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan sakai da fararen hula yayin harin Filato? Gaskiya ta fito

Police
Yan daba sun kashe mutune biyu a Neja. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

‘Yan ta’addan sun far wa mazauna yankin tare da kai harin kan-mai-uwa-da-wabi kan shaguna da dama a yankin a ranar Juma’a.

Jaridar the Cable ta tabbatar da cewa kakakin ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma tabbatar da cewa 'yan sanda sun yi nasarar kama mutane shida da aikata laifin.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan na kokarin ganin ta cafke sauran wadanda ake zargi da suka gudu.

Jawabin kakakin 'yan sanda

“An kashe mutum biyu. Tawagar ‘yan sandan da ke sintiri sun kai dauki inda suka kama mutane kusan shida. Sai dai ana ci gaba da sa ido da nufin kamo sauran miyagu da suka gudu.”

-Wasiu Abiodun, Kakakin 'yan sandan jihar Neja

Umarnin gwamnan Neja, Umar Bago

Da yake magana da manema labarai yayin bikin durbar na shekara-shekara a ranar Lahadi, gwamna Bago ya ce ya ba da umarnin harbin 'yan daba nan take ga jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Daliban jami'ar tarayya ta Gusau da aka sace sun samu 'yanci

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa gwamnan ya dora alhakin tashin hankalin a kan masu aikin hakar ma’adinai, ya kara da cewa an dauki matakai don shawo kan lamarin.

Gwaman ya kuma sanar da kafa dokar ta-baci kan duk wani dan daba da aka samu a cikin jihar.

Ya kuma kara da cewa duk wani gida da aka samu matsugunin ‘yan daba ne a ruguje shi, kuma duk wani dan daba da aka samu da makami a yi maganinsa yadda ya kamata.

An kai hari jihar Neja

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kauyen Tegina a jihar Neja

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa maharan sun shiga garin a kan babura suna ta harbe-harbe kuma sun hallaka al'umma da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel