Binciken Ganduje: Jigo a APC, Kwankwaso Ya Magantu Bayan Fitowa Daga Kotu, Ya Fadi Matsayarsa

Binciken Ganduje: Jigo a APC, Kwankwaso Ya Magantu Bayan Fitowa Daga Kotu, Ya Fadi Matsayarsa

  • Jigon jam'iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso ya caccaki gwamnatin jihar Kano kan tuhumar Abdullahi Umar Ganduje
  • Ilyasu Kwankwaso ya ce gwamnatin ba ta shirya ba ko kadan inda ya ce suna kokarin shigowa jam'iyyar APC ne shi ne suka ta da rigima
  • Na hannun daman Ganduje ya bayyana haka ne a yau Laraba 17 ga watan Afrilu bayan fitowa daga kotu kan tuhumar tsohon gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da tuhumar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi martani.

Ilyasu Kwankwaso ya ce gwamnatin jihar Kano ba a shirye ta ke ba kan wannan shari'a da ta dauko.

Kara karanta wannan

Jimami yayin da tsohon Sanata Ibrahim ya riga mu gidan gaskiya, bayanai sun fito

Jigon APC, Kwankwaso ya yi martani kan binciken Ganduje a Kano
Jigon APC, Ilyasu Kwankwaso ya ce gwamnatin Kano ba ta shirya ba a binciken Abdullahi Ganduje. Hoto: Musa Ilyasu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Wane zargi Kwankwaso ya yi wa Ganduje?

Jigon APC ya bayyana haka ne bayan fitowa daga kotu a yau Laraba 17 ga watan Afrilu a wani faifan bidiyo yayin hira da Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya na shirin shiga jam'iyyar APC ne shiyasa ya ke kokarin turo Abba Kabir a watan biyar kafin ya shiga.

Ya ce hakan kokari ne na kawo rigima a jam'iyyar domin ya samu hanyar shigowa inda ya ce su na jiransa ya shigo.

"Gwamnatin jihar Kano ba a shirye ta ke ba, ba ta shirya ba, da gan-gan ta ke yi."
"Kwankwaso ya na kokarin shigowa jam'iyyar APC, zai fara turo Abba a watan biyar shiyasa ya ke kokarin kawo rigima domin haka babu abin da zai fitar da mu."
"Idan sun shiga muna nan muna jiransu saboda Ganduje shi ne shugaban jam'iyyar APC kuma shi zai karbe su a jam'iyya."

Kara karanta wannan

Ana shirin gurfana gaban kotu, Ganduje ya aika muhimmin sako ga gwamnatin Kano

- Musa Ilyasu Kwankwaso

Musa Kwankwaso ya fadi 'shirin' Kwankwasiyya

Ilyasu Kwankwaso ya kara da cewa daman sun fada a baya Kwankwaso ya na yi wa Tinubu aiki ne.

Ya kuma gargadi cewa ya kamata a kula saboda abin da Kwankwaso ya yi wa Goodluck da Buhari da Atiku haka zai yi wa Tinubu.

Ganduje ya magantu kan shari'ar da ake yi

Kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bugi kirji kan tuhumar da da gwamnatin jihar Kano ke yi.

Ganduje ya ce ko kadan babu abin da zai girgiza shi kan tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar Kano ke yi kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel