N585m: Jama'a Sun Taso EFCC da Tinubu a Gaba Saboda An Ji Tsit a Binciken Edu

N585m: Jama'a Sun Taso EFCC da Tinubu a Gaba Saboda An Ji Tsit a Binciken Edu

  • 'Yan Najeriya sun garzaya dandalin soshiyal midiya domin bayyana ra'ayoyinsu kan shiru da EFCC da Shugaban kasa Bola Tinubu suka yi da badakalar Betta Edu
  • Yayin da wasu suka ce tuni aka rufe batun, wasu sun nuna rashin jin dadinsu, suna masu cewa talaka kadai ake hukuntawa a Najeriya
  • 'Yan Najeriya na son sanin ko Shugaba Tinubu zai tsige Betta Edu, ministar da ta taka muhimmiyar rawar gani wajen ganin ya zama Shugaban kasar Najeriya na 16 a 2023

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

A ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 'yan Najeriya sun yiwa hukumar EFCC da fadar shugaban kasa wankin babban bargo sosai dangane da shirun da suka yi kan badakalar dakatacciyar ministan jin kai, Betta Edu.

Kara karanta wannan

Duk da gwamnati ta dauki mataki, farashin gas din girki ya sake lulawa har ya haura N1300

Yayin da wasu 'yan Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu kan lamarin, wasu 'yan kadan sun bayyana cewa basu yi tsammanin za a yiwa lamarin rikon sakainar kashi ba duba ga matsayin wacce abin ya shafa.

'Yan Najeriya sun caccaki Tinubu kan gum da ya yi a badakalar Edu
'Yan Najeriya na son sanin inda aka kwana a badakalar Betta Edu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Haka kuma, sun ce basu yi tsammanin haka ba idan aka yi la'akari da alkawarin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka a lokacin yakin neman zabensa cewa zai ci gaba daga inda magabacinsa ya tsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa a watan Janairun 2024, EFCC ta tsitsiye Edu. An dakatar da ita kan zargin karkatar da kudi sama da naira miliyan 585 na jama'a zuwa wani asusu mai zaman kansa.

Haka kuma, kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fadawa manema labarai cewa an bayar da belin Edu, amma bai bayyana sharuddan da aka bi wajen sakin nata ba.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, daga EFCC har fadar shugaban kasa babu wanda ya ba 'yan Najeriya karin bayani kan lamarin, watanni biyu bayan dakatar da ita.

Betta Edu: Me 'yan Najeriya ke cewa?

Kamar kullum, 'yan Najeriya sun garzaya dandalin X su bayyana ra'ayoyinsu kan batun. Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martaninsu a kasa:

@LawalOlabisi4 ya rubuta:

"Haka za a yi kowa ya manta da batun sannan a ci gaba da harkoki, kasa mai wayo."

@KabiruMisali ya yi martani:

"Babu wanda ke son alakanta kansa da kaskantattu Betta Edu da Halima Shehu."

@Tammyxxx3 ta yi martani:

"Da zarar kana APC to an yafe maka dukkan zunubanka."

@iykeplc ya ce:

"Me kuke tsammanin ji ko gani?"

Gbajabiamila: Abbas ya magantu kan badakalar Edu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai, ya bukaci hukumomin tsaro da su fara bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake zargin Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya aikata.

Abbas ya yi kiran ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, yayin wani taron manema labarai kan halin da kasar ke ciki a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel