Betta Edu: EFCC Ta Fadi Inda Aka Kwana Game da Tuhumar Tsohuwar Ministar Jin Ƙai

Betta Edu: EFCC Ta Fadi Inda Aka Kwana Game da Tuhumar Tsohuwar Ministar Jin Ƙai

  • Hukumar EFCC ta magantu game da inda aka kwana kan tuhumar da ake yi tsohuwar ministar jin ƙai Betta Edu da Halima Shehu
  • Halima Shehu ita ce tsohuwar shugabar shirin NSIPA, kuma Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da ita da Ministar kan zargin rashawa
  • EFCC ta ce ya zuwa yanzu ta karbo Naira biliyan 30 daga wasu asusun bankuna 50 da take binciken da suka shafi Edu da Shehu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta ce ta kwato N30bn yayin da take ci gaba da bincike asusun bankuna 50 a binciken tsohuwar ministar jin kai Betta Edu da ake yi.

EFCC ta magantu kan binciken da take yi wa Betta Edu da Halima Shehu
Ola Olukayode ya ce 'yan Nijeriya su kara hakuri kan binciken da ake yi wa Betta Edu. Hoto: @edu_betta, @NSIPAgency
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto EFCC ta ce bincike ta shafi har da tsohuwar shugabar shirin ba da tallafi ga marasa galihu na gwamnatin tarayya (NSIPA), Halima Shehu.

Kara karanta wannan

Tuhuma kan aikata laifuffuka 26, Emefiele ya isa kotu, ya gurfana gaban alkali

Tinubu ya dakatar da Betta Edu, Shehu

A watanni uku da suka wuce ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Edu da Shehu kan zargin tafka almundahana a ofisoshinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya kuma dakatar da shirin NSIPA gaba daya tare da umurtar EFCC ta gudanar da bincike kan dakatattun matan.

Bayan watanni uku ana bincike, daraktan hukumar EFCC, Ola Olukayode, wanda ya bayyana hakan ya ce hukumar suna samun ci gaba sosai a kan binciken.

"EFCC ta karbo N30bn" - Olukoye

Jaridar Vanguard ta rahoto Olukoye ya bayyana hakan ne a a cikin mujallar hukumar da ake fitarwa wata-wata mai suna EFCCAlert.

"Muna da wasu ayyukan da aka shafe shekara ba a kammala su ba, wannan kuma kun ga makonni shida ne da muka fara bincike a kan lamarin.

Kara karanta wannan

"Ka mayar da Pam matsayin shugaban NCPC": Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu

"Muna fatan 'yan Nijeriya za su kara hakuri, su bamu damar gudanar sahihin bincike tunda yanzu mun kwato N30bn, mun mika wa gwamnati."

Daraktan hukumar ya ce zuwa yanzu 'yan Nijeriya sun ga kokarin da EFCC ke yi, la'akari da adadin mutanen da ake bincike da kudade ko kadarorin da aka kwato.

Sabani tsakanin Edu da Halima

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa an samu sabani tsakanin Halima Shehu, tsohuwar shugabar shirin NSIPA da Betta Edu, tsohuwar ministar jin kai.

Yayin da aka dakatar da Shehu daga shugabar NSIPA, hukumar EFCC ta bankaɗo wasu laifuffuka da ake zargin sun shafi Edu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel