Hotunan da ya tabbatar da cewa an sace yan matan Chibok
Lura daga Edita: bukatar kungiyar yan Boko Haram na kwanan nan ga gwamnatin tarayya ta wani bidiyo da son chanza yan matan Chibok da mayakan boko haram ya isa nuna cewa yan matan na cikin hadari, amma abun mamaki yan Najeriya da dama sun dauki dukkan satan a matsayin zamba.
A wani bidiyo, wani mayakin kungiyar Boko Haram da ya boye fuskar sa ya bayyana a gaban sama da yan mata 50 dake sanye da hijab ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta saki mayakansu domin yan matan. Daya daga cikin yan matan wacce ta kira sunanta da Esther (Dorcas) Yakubu tayi Magana cikin harshen hausa, ta bukaci gwamnati da ta cece su ta kuma ba iyayenta hakuri da su kwantar da hankalinsu.
Duk da sabon bidiyon da sauran labarai, wasu mutane da aka sani kamar gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ci gaba da cewa babu wasu yan mata da aka sace a Chibok kuma cewa satan da ake ikirari zamba ne.
A ranar 14 ga watan Afrilu na shekara 2014, an sace yan mata 276 daga makarantar sakandari gwamnatin a garin Chibok dake jihar Borno. Bisa ga rahoto, dan ta’addan yayi shiga cikin kayan sojoji, ya kuma jagoranci yan matan zuwa motar da yaudarar cewa suna cetonsu ne daga harin Boko Haram. Wasu daga cikin yan matan sun tsere kafin su kai masaukin yanta’addan.
KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun saka wuta a kauyen Borno; an sace mata
An gayyaci Amina Ali, daya daga cikin yan matan Chibok da jami’an tsaro suka ceto a ranar 16 ga watan Mayu ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin yan matan sun mutu.
Yan ta’addan sun saki bidiyo dake nuna yan matan da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar, ya tabbatar da cewa yan matan na hannunsu. Haka kuma sabon bidiyon da suka saki ya nuna haka.
Duk da wannan wasu mutane sun dage cewa satar karya ne.hotunan nan zasu canza wa wadannan tunanin su.
Asali: Legit.ng