Da Gaske An Saki Nnamdi Kanu Bayan An Duba Lafiyarsa? DSS Ta Yi Karin Haske

Da Gaske An Saki Nnamdi Kanu Bayan An Duba Lafiyarsa? DSS Ta Yi Karin Haske

  • Shugaban ƙungiyar ƴan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, yana tsare a hannun hukumar ƴan sandan farin kaya ta ƙasa (DSS)
  • Hukumar ita ce ta bayyana hakan bayan daga ƙarshe ta bar Kanu ya gana da likitocinsa domin duba lafiyarsa a ƙarshen mako
  • Hukumar DSS ta tabbatar cewa har yanzu Kanu yana tsare a hannunta kuma ba a sake shi ba kamar yadda ake yaɗa jita-jita

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ba a saki shugaban ƙungiyar ƴan aware ta 'Indigenous People of Biafra' (IPOB), Nnamdi Kanu, daga hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ba.

Wani majiya na kusa da hukumar DSS ya bayyana cewa a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli, hukumar ta bi umarnin wata babbar kotun tarayya na barin likitocin Kanu su duba lafiyarsa, amma har yanzu yana tsare a hannunta, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dum-Dumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Manyan Alkalai 2 a Najeriya Suka Kwanta Dama

DSS ta magantu kan sakin Nnamdi Kanu
DSS ta yi karin haske kan sakin Nnamdi Kanu Hoto: @Biafrantweets
Asali: Twitter

Lauyan Kanu ya tabbatar cewa shugaban na IPOB ya koma hannun DSS

Lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya gayawa jaridar The Punch ta wayar tarho cewa shugaban na IPOB wanda yake tsare tun shekarar 2021, an bar shi ya gana da likitocinsa sannan ya koma wajen DSS inda ake ci gaba da tsare shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ejiofor ya bayyana cewa:

"An duba lafiyarsa, bayan an kammala masa gwaje-gwaje an mayar da shi hannun DSS."

Sai dai, lauyan bai yi ƙarin haske ba kan halin rashin lafiyar Kanu ba, da sauran wasu abubuwa na daban da suka shafi ɗaurin da aka yi masa.

DSS ta saki Nnamdi Kanu domin a duba lafiyarsa bayan umarnin kotu

Barr. Ifeanyi Ejiofor, lauyan Nnamdi Kanu, ya bayyana cewa an duba lafiyar shugaban ƴan awaren ne a asibitin da yake so.

Kara karanta wannan

Emefiele: Peter Obi Ya Dau Zafi Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu, Ya Bayyana Matakin Da Ya Dace a Dauka

Ejiofor ya bayyana cewa Kanu ya gana da likitocinsa ne a wani asibiti wanda ba na hukumar DSS ba.

Obi Ya Yi Martani Kan Takaddamar Jami'an DSS Da NCoS

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi Allah wadai da abinda ya kira da abun kunya wanda jami'an DSS da na NCoS suka yi a gaban kotu kan Emefiele.

Obi ya bayyana cewa abinda jami'an suka yi abun kunya ne wanda zai zubar da ƙimar Najeriya a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel