Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Lokacin da Za Ta Kawo Karshen Yan Bindiga a Najeriya, Ta Ce In Sha Allah

Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Lokacin da Za Ta Kawo Karshen Yan Bindiga a Najeriya, Ta Ce In Sha Allah

  • Najeriya na fama da matsalolin tsaro iri daban-daban wanda ya kunshi garkuwa da mutane, ta'addanci da ƴan aware
  • Bayanai sun nuna cewa kusan kowane yanki a Najeriya yana fama da wata matsala da take barazana ga tsaro da zaman lafiya
  • Sai dai a yanzu karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya jaddada kurin Bola Tinubu na kawo karshen rashin tsaro a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta lashi takobin murkushe matsalar tsaro gaba ɗaya daga nan zuwa 2024.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta fahimci dukkan kalubalen tsaron da suka hana jama'a zaman lafiya da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Gwamnatin Tinubu Ya Bayyana Lokacin da Za Ta Murkushe Matsalar Tsaro a Najeriya Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Zamu kawo karshen matsalar tsaro - Gwamnatin APC

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa wadda aka wallafa ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya jaddada kwarin guiwar cewa matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka na magance matsalolon tsaro zasu taimaka wajen kawo karshen hare-haren ƴan bindiga.

Karamin ministan ya ce:

"In sha Allahu, abinda muke tunani kuma muke fata idan Allah ya yarda daga nan zuwa sabuwar shekarar 2024 da zamu shiga, kamar watan 11 zamu shawo kan matsalar tsaro."

Bugu da ƙari, Mawalle ya ce gwamnonin jihohin da ke fama da rashin zaman lafiya suna aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya domin kawo karshen lamarin.

A cewarsa, shi da Ministan tsaro, Abubakar Badaru duk tsoffin gwamnoni ne kuma sun san illar halin rashin tsaron da ake ciki, kuma zasu magance ta.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan Arewa ya sa labule da babban hafsan tsaro na ƙasa kan muhimmin abu 1

Ayyukan ta'addancin yan bindiga, garkuwa da mutane, hare-haren Boko Haram/ISWAP da kuma ƴan aware IPOB na cikin kalubalen tsaron da ake fama da su a Najeriya.

Dakarun Sojoji Sun Sheke Dan Bindiga a Kaduna

A wani rahoton kuma Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan bindiga masu tayar da ƙayar baya a jihar Kaduna

Dakarun sojojin sun halaka wani ɗan bindiga ɗaya a Sabon Birni cikin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar a wani kwanton ɓauna

Asali: Legit.ng

Online view pixel