Hotunan Yadda ’Yan Sanda Suka Kwamushe ’Yan Daba 61 da ke Tada Zaune Tsaye a Jihar Kano

Hotunan Yadda ’Yan Sanda Suka Kwamushe ’Yan Daba 61 da ke Tada Zaune Tsaye a Jihar Kano

  • 'Yan daba sun shiga hannun 'yan sanda a daidai lokacin d ake ci gaba da yakar masu tada zaune a Kano
  • Rahoto ya nuna irin aikin da 'yan sandan suka yi har ta kai ga kame wadanda ake zargi da aikata laifukan
  • Jihar Kano da sauran jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da 'yan daba masu kwacen waya

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kame wasu 'yan daba 61 a masarautu biyar na jihar bisa zarginsu da aikata dabanci a fadin masarautun.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da bukukuwan sallah karama, inda su kuwa suke kokarin tada zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: 'Yan sanda a Kano sun kama mutum 54 masu yunkurin hargitsa hawan sallah

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta shafinsa na Facebook, ya ce an kama su ne a tsaka da lokutan bukukuwan sallah.

'Yan sandan Kano sun kame 'yan daba ana bikin sallah
An kama masu tarwatsa bikin sallah a Kano | Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani daga 'yan sanda kan kame 'yan daba

A cewarsa:

"Rundunar 'yan sandan jihar Kano, a kokarinta na yaki da dukkan nau'ikan dabanci da kuma tabbatar da an yi bikin sallah lafiya, ta kame wasu 'yan daba 61 wanda ya kai ga 115 kenan yanzu daga yankunan masarautu biyar na jihar.
"Kwamishinan 'yan sanda Mohammed Usaini Gumel ya kuma yabawa dukkan hukumomin tsaro na hadin gwiwa da suke aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya a jihar."

Kayayyakin da aka kwace a hannun 'yan daban

A hotunan da wakilin Legit ya gani, akwai matasa dauke da makamai da sauran nau'ikan kayayyakin aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Daga ciki, akwai adduna da wukake da ke nuna alamun 'yan daban ka iya illata duk wanda suka hadu da shi a irin wannan shirin da suka yi.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano na yawan fama da aikin kamo 'yan daba tare da gurfanar da su a gaban kotu, amma an ce, idan dambu ya yi yawa, bai jin mai.

Kalli hotunan a nan:

Yadda aka nemi wasu 'yan daba ruwa a jallo a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bazama neman wasu 'yan daba uku da suka addabi mutane ruwa a jallo.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Muhammad Gumel shi ya tabbatar da haka a ranar Laraba 2 ga watan Agusta.

Ya ce rundunar ta ware N100,000 ga duk wanda ya taimaka wurin ba da bayanin sirri don kama su a cikin mako daya, cewar Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel