'Yan Ta’addan ISWAP Sun Kashe Dan Sandan da Suka Yi Garkuwa da Shi a Borno
- Kungiyar 'yan ta'addan ISWAP, masu rajin kafa daular Muslunci a yammacin Africa, sun kashe dan sanda a jihar Borno
- 'Yan ta'addan sun kama dan sandan ne tare da iyalensa lokacin da suke ƙoƙarin dawowa gida hutun sallah ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu
- Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun saki iyalan nasa kafin daga bisani suka kashesa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Kungiyar da Ske da’awar kafa daular Musulunci a yammacin Afirka (ISWAP) ta kashe wani dan sanda da ta yi garkuwa da shi a jihar Borno.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa 'yan ta'addan sun yi garkuwa da dan sandan ne ranar Lahadi 7 ga watan Afrilu.
Wurin da aka kama dan sandan
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama dan sandan ne a lokacin da yake tafiya gida hutun sallah tare da matarsa da ‘ya’yansa a kan hanyar Dambuwa zuwa Biu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga baya an tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’adda ne da ake fargabar ‘yan ƙungiyar ISWAP ne suka yi awon gaba da dan sandan tare da iyalansa a kusa da yankin Shokotoko da ke da tazarar kilomita 73 da kudancin Dambuwa.
Sai dai kuma da yammacin ranar an sako matar da ‘ya’yansa, yayin da ‘yan ta’addan suka kashe dan sandan, cewar jaridar The Guardian
An kashe dan sanda a Ribas
A wani rahoton kuma, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani sufeton ‘yan sanda tare da sace bindigarsa, da kuma hular aikinsa a jihar Ribas.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mummunan al’amari ya afku ne a daren Juma’a 25 ga watan Agusta a kusa da wani shahararren otal a Oroworukwo-Olu Obasanjo, a birnin Fatakwal
Wata majiya ta ce tsagerun masu kisan gillar sun zo ne a kan wata mota kirar Toyota Corolla 2005 mai launin toka
An kashe dan sanda a Imo
Har ila yau kun ji cewa wasu tsagerun 'yan bindiga sun kashe Augustine Ukegbu, sufeton dan sanda yayin da yake hutu da iyalansa a Imo.
An tattaro cewa makasan sun farmaki gidan sufeton dan sandan sannan suka yi garkuwa da shi a wata bakar Jeep kirar Lexus
Asali: Legit.ng