Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun kai hari Damboa da yamman nan, sun katse layukan sadarwa

Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Damboa dake jihar Borno da yammacin Asabar, 2 ga watan Oktoba, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun dira garin ne misalin karfe 5 na yamma.

Majiya ta bayyana cewa jim kadan bayan dirarsu Damboa, layukan sadarwa suka katse.

Rahoton ya kara da cewa Sojoji na artabu yanzu haka da yan bindigan.

Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun kai hari Damboa da yamman nan, sun katse layukan sadarwa
Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun kai hari Damboa da yamman nan, sun katse layukan sadarwa
Source: Original

Source: Legit Nigeria

Online view pixel