Gwamnan Arewa Ya Yi Alkawarin Cigaba da Raba Tallafi Ga Talakawa Har Bayan Ramadan

Gwamnan Arewa Ya Yi Alkawarin Cigaba da Raba Tallafi Ga Talakawa Har Bayan Ramadan

  • Gwamna Bala Mohammed ya yi alƙawarin cewa zai ci gaba da tallafawa mutane da kayan abinci har bayan watan azumin Ramadan a Bauchi
  • Ƙauran Bauchi ya kuma ja hankalin al'ummar musulmi su kaunaci juna kuma su yi koyi da kyawawan ɗabi'un Annabi Muhammad SAW
  • Bala Mohammed ya faɗi waɗannan kalaman ne a filin idi jim kaɗan bayan kammala Sallar idin ƙaramar sallah ranar Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da rabawa mutane tallafi har bayan wucewar watan Ramadan.

Ƙauran Bauchi ya ce za a ci gaba da rabawa talakawa da mabuƙata tallafin ne domin magance wahalhalun rayuwa da aka shiga a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnatin Bauchi za ta ci gaba da agaza wa al'umma har bayan Ramadan Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Facebook

Gwamna Bala ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai jim kaɗan bayan idar da Sallar idin Eid-el-Fitr a Bauchi ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matsin tattalin arzikin da aka shiga na buƙatar gwamnatoci a kowane mataki su haɗu su masa taron dangi domin tsamo al'umma daga halin da suka shiga.

A cewarsa, bayan gwamnati akwai buƙatar ƙungiyoyi masu zaman kansu su taimaka domin rage wa mutane raɗaɗi, jaridar Leadership ta ruwaito.

Gwamna Bala ya rabawa ma'aikata N10,000

Bala Muhammed ya ce kyautar N10,000 da gwamnatinsa ta bai wa kowane ma'akaci a matakin jiha da ƙananan hukumomi a matsayin goron sallah shi ne karo na farko a tarihi.

Bisa haka gwamnan ya yi kira ga dukkan ma'aikatan jihar da su biya wannan alheri ta hanyar ƙara dagewa a ayyukansu.

Ya kuma yi kira ga ɗaukacin musulmi da su ƙaunaci juna kuma su yi riƙo da koyarwar addinin Musulunci, sannan su kwatanta koyi da halayen Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

Mohammed ya buƙaci al’ummar musulmi da su karfafa alakarsu da junansu, su sanya soyayya da afuwa a tsakaninsu don jawo albarkar Allah, PM News ta ruwaito.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna Bauchi kuma sun bayyana cewa wannan abu ne mai kyau, suna fatan Allah ya ba shi ikon cika wannan alƙawari.

Yusuf Baba ya shaida mana cewa da farko suna godewa Allah da ya ba su ikon ganin watan Ramadan har ƙarshensa lafiya da fatan Allah ya maimaita.

A cewarsa, duk da bai samu tallafin gwamnafi ba amma ya san waɗanda suka samu kuma tallafin da taimaka masu matuƙa saboda halin da ake ciki.

"Gaskiya tallafin yana taimakawa mutane da yawa, amma ni a ganina gara a sauke farashin kayayyaki, kowa ya siya da kuɗinsa. Game da alkawarin gwamna kuma muna fatan Allah ya ba shi ikon cikawa," in ji shi.

Haka nan wani mai suna Isiyaka Sani ya ce duk wannan tallafin ba shi ne matsalar ba, gwamnati ta dawo da komai kamar baya shi ne kaɗai mafita.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya faɗi watan da yan Najeriya za su fita daga ƙangin tsadar rayuwa a 2024

Gwamnonin da suka tsawaita hutun Sallah

Legit Hausa ta tattaro muku jerin gwamnonin da suka ƙara kwanakin da tsawaita hutun ƙaramar Sallah har zuwa ranar 12 ga watan Afrilu.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu, inda ta bayyana hutun kwana biyu daga bisani ta ƙara ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel