Rikicin Numan: Kungiyar Kirista da majalisar musulmin sun yi musayar zafafan kalamai ga junan su
Kungiyar nan ta addinin Kirista reshen Adamawa dake a Arewa maso gabashin kasar nan ta yi Allah-wadai da kalaman Sarkin Musulmi a kan rikicin garin Numan inda aka yi wa makiyaya Fulani kisan kiyashi a cikin satin da ya gabata inda kungiyar ta nuna cewa kalaman nasa na iya haifar da wani sabon rikici.
Mun samu dai cewa a kwanan baya Sarkin Musulmi ya fito fili ya yi gargadin cewa kada fa a dauki hakurin makiyaya a matsayin rauni daga gare su. Sai dai shugaban na kungiyar Kiristocin, Dakta Stephen Dami Manza ya bayyana irin wannan kalaman a matsayin wadanda basu dace su fito daga bakin shugaban addini ba inda ya nuna cewa rikicin tsakanin Fulani ne da 'yan kabilar Bachama don haka a cewarsa, ba ya da alaka da addini.
KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya bayyana wadanda ya kamata su yaki Boko Haram
Legit.ng haka zalika ta samu cewa a dayan bangaren Shugaban na Majalisar Musulmai a jihar ta Adamawa dake arewacin kasar nan, Alhaji Abubakar Magaji ya mayar da raddi ga Shugaban na kungiyar Kiristocin inda ya bayyana cewa manufar rikicin shi ne, na shafe mabiya addinin Musulunci da makiyaya daga yankin inda ya kuma bayyana goyon bayan sa ga kalaman na Sarkin Musulmi.
Ya kara da cewa dole ne fa ya furta wadannan kalaman saboda an jima ana kashe Musulmi da makiyaya amma kuma gwamnati ba ta dauki mataki ba.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin daya gabata ne dai aka kaiwa fulani dake a ganin na Numan hari tare da kashe da dama daga cikin su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng