Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano

Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano

Gwamnatin tarayya (FG) ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin jihar Kano.

Tallafin na daga cikin kokarin gwamnati na ragewa jama'a radadi da matsin da suka shiga sakamakon bullar annobar korona.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya fitar a shafinsa na tuwita da yammacin ranar Lahadi.

Ministar walwala, jin kai da bayar da tallafi, Sadiya Umar Farouk, ta damka tallafin kayan abincin ga gwamnan jihar Kaduna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwar ba ta bayyana lokaci ko a wurin da aka damka tallafin ga gwamnatin Kano ba.

Kazalika, gwamnatin Kano ba ta fitar da sanarwa a kan bayar da tallafin ba har ya zuwa wannan lokaci.

Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano
Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano
Source: Twitter

Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano
Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano
Source: Twitter

Daga jihar Katsina mai makwabtaka da Kano, gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya bayar da umarnin sassauta dokar kulle jihar Katsina na tsawon mako guda.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina (SSG), Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

Ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar sassauta dokar ne bayan ganawarta da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar yayin taron da ta saba gudanarwa.

Inuwa ya bayyana cewa sassauta dokar kullen za ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.

Ya ce za a sassauta dokar ne a cikin kananan hukumomin jihar, amma kuma dokar hana bulaguro zuwa wasu kananan hukumomin ta na nan daram.

Ya bayyana cewa gwamna Masari ya umarci sarkin Daura da na Katsina da sauran manyan masu rike da sarautar gargajiya a kan su tabbatar da cewa dagatai sun zauna a garuruwansu tare da jama'arsu yayin bukukuwan Sallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel