'Yan Sanda da Yan Shi'a Sun Yi Mummunar Arangama, Mutane Sun Mutu a Arewa, Bidiyo Ya Fito

'Yan Sanda da Yan Shi'a Sun Yi Mummunar Arangama, Mutane Sun Mutu a Arewa, Bidiyo Ya Fito

  • Jami'an ƴan sanda da ƴan shi'a sun yi arangama ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 yayin da suka fito muzaharar ranar Quds a Kaduna
  • Ƴan shi'ar sun fito da yawa a Kaduna amma ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa su saboda wasu daga cikin suna ɗauke da makamai
  • Makamancin haka ta faru a Zaria, inda wani ganau ya shaidawa Legit Hausa cewa mutane sun shiga tashin hankali bayan jin karar harbi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - An shiga tashin hankali a shataletalen Katsina da ke titin Ahmadu Bello Way a cikin birnin Kaduna yayin da ƴan shi'a suka fito ranar Quds.

Lamarin ya fara ne yayin da dakarun ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa taron kungiyar IMN ta ƴan uwa Musulmi IMN wadanda aka fi sani da ƴan shi'a.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka tantiran 'yan ta'adda 3 a jihar Arewa

Yan sanda.
An yi tashin hankali tsakanin ƴan sanda da ƴan shi'a a Kaduna Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

‘Yan shi’an sun gudanar da muzahara ne a cikin birnin ranar Juma’a 5 ga watan Afrilu, inda kamar yadda aka saba, aka samu rudani da tashin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton Daily Trust, ƴan shi'a sun yi ikirarin cewa jami'an ƴan sanda ne suka tarwatsa masu taron da suke yi na lumana. An ji ƙarar harbe-harben bindiga.

Ƴan shi'a dai sun saba fitowa muzahara a kowace ranar Jumu'a ta karshe a watan Ramadan, suna kiran wannan rana da ranar Qudus.

Jaridar Vanguard ta ruwaito wani ganau na cewa:

"An yi wa kowane ɓangare illa, ƴan shi'a biyu ake fargabar sun mutu. Haka nan kuma wasu daga cikin jami'an ƴan sanda sun ji raunuka kuma tuni aka kai su asibiti."

Duba bidiyon abin da ya faru.

Ƴan sanda sun yi magana

Kara karanta wannan

Kaduna: An bayyana adadin ƴan shi'a da suka mutu a rikicin da ya faru, ƴan sanda sun yi raddi

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya ce da safiyar Jumu'a ƴan shi'a suka fito ɗauke da mugayen makamai kana suka fara farmakar mutanen gari.

Ya ce da sunan taron muazahara, ƴan shi'a sun farmaki jama'a ba gaira babu dalili, sun kuma ji wa wasu ƴan sanda raunuka.

A cewarsa, yanzu haka sun kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi kuma za a gurfanar da su kamar yadda doka ta tanada.

Ƴan shi'a sun jawo matsala a Zaria

Wani mai suna Aliyu Yusuf ya shaidawa Legit Hausa cewa kusan irin haka ta faru a kusa da kasuwar Sabon Gari, Zariya yayin da je sayo kaya ranar Jumu'a.

Ya ce:

"Wallahi da kyar na sha, gudu na yi na gaske, babur ɗina ma sai daga baya na ɗauko shi. Ba zan iya faɗin ga abin da ya haɗa ƴan shi'a da jami'an tsaro ba, mun dai ji bindiga na tashi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a wani sabon hari a jihar Arewa

"Daga nan fa muka fara gudun neman tsira, kuma su ƴan shi'a suna ɗauke da duwatsu da wasu abubuwa haka, ni dai kam ban ma sayo abin da ya kai ni ba, na dawo gida."

Ɗan majalisa ya sha da ƙyar

A wani rahoton kuma wasu ƴan daba da ake zargin turo su aka yi sun farmaki ɗan majalisar wakilan tarayya, Cif Philip Agbese a jihar Benuwai.

Ganau ya bayyana cewa ƴan daban dauke da makamai sun farmaki ɗan majalisar ne a wurin taron bikin Easter a mazaɓarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel