Kaduna: An Bayyana Adadin Ƴan Shi'a da Suka Mutu a Rikicin da Ya Faru, Ƴan Sanda Sun Yi Raddi

Kaduna: An Bayyana Adadin Ƴan Shi'a da Suka Mutu a Rikicin da Ya Faru, Ƴan Sanda Sun Yi Raddi

  • Ƴan shi'a sun yi ikirarin cewa ƴan sanda sun kashe masu mutum huɗu yayin arangamar da suka yi a cikin birnin Kaduna ranar Jumu'a
  • Aliyu Tirmizy, ɗaya daga cikin jagoroin ƴan shi'a ya ce suna cikin zanga-zangar lumana ƴan sanda suka far masu
  • Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Kaduna ya ce babu wanda aka kashe kuma idan ƴan shi'ar da gaske suke yi su bayyana gawarwakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Kungiyar musulmai ta IMN wadda aka fi sani da Shi'a ta yi zargin cewa jami'an 'yan sanda sun kashe mambobinta hudu a ranar Juma'a a jihar Kaduna.

Da yake magana da manema labarai bayan faruwar lamarin, Aliyu Tirmiziy, daya daga cikin shugabannin IMN, ya ce wasu ƴan shi'a 20 kuma sun jikkata, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka tantiran 'yan ta'adda 3 a jihar Arewa

Yan sanda.
Yan shi'a sun yi zargin an kashe masu mutum 4 a Kaduna Hoto: PoliceNG
Asali: Getty Images

Tirmiziy ya ce sun fito ne su yi zanga-zanga domin nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu a lokacin da 'yan sanda suka zo suka tarwatsa su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu kan fito a ranar Juma’ar karshe na kowane watan Ramadan don mu yi zanga-zangar lumana tare da nuna goyon bayanmu ga al’ummar Palastinu kan cin zarafin da ake yi musu a duniya.
"Galibi mu kan yi tattaki cikin lumana amma a wannan karon da za mu fara sai ‘yan sanda suka zo suka jefa mana hayaki mai sa hawaye suka fara harbe-harbe, garin haka suka kashe mana mutum hudu yayin da 20 suka jikkata.”

- Aliyu Tirmiziy.

Lamarin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin Kaduna, musamman ‘yan kasuwar da ke kan titin Ahmadu Bello, inda suka yi gaggawar rufe shaguna suka nemi wurin tsira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a wani sabon hari a jihar Arewa

Ƴan sanda sun mayar da martani

Sai dai Mansir Hassan, kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, ya ce babu wanda ya rasa ransa, yana mai cewa ba a yi amfani da harsashi mai rai wajen tarwatsa masu zanga-zangar ba.

Ya ce jami’an ‘yan sanda uku sun ji raunuka sakamakon abin da ya faru kuma yanzu haka an kwantar da su suna karbar magani a wani asibiti.

"Mun samu labarin ƴan shi'a za su yi gagarumar zanga-zanga, hakan ya sa muka girke jami'an mu a wurare masu muhimmanci musamman Ahmadu Bello Way.
"Daga ganin ƴan sanda, kawai ƴan shi'an suka fra jefansu da duwatsu da bindigar cikin gida,wanda hakan ya raunata mutum uku, suna kwance a asibiti."

- Mansir Hassan.

Yan sanda sun kama mutum 8

Kakakin ‘yan sandan ya ce an kama mutane takwas da ake zargi, inda ya kara da cewa an kwato bindigu na gida guda uku da wasu makamai.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da ƴan shi'a sun yi mummunar arangama, mutane sun mutu a Arewa, bidiyo ya fito

Hassan ya ƙalubalancin ƴan shi'a cewa idan suna ikirarin an kashe masu mutum huɗi to su fito da gawarwakinsu kowa ya gani, cewar rahoton Leadership.

Yan sanda sun samu nasara a Kano

A wani rahoton kuma Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a cikin watan Maris.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daga cikin waɗanda aka kama har da masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel