Sabuwar Matsala Ta Kunno Ga Alhazan Najeriya Kan Ƙarin Kuɗin Hajjin 2024, NAHCON Ta Magantu

Sabuwar Matsala Ta Kunno Ga Alhazan Najeriya Kan Ƙarin Kuɗin Hajjin 2024, NAHCON Ta Magantu

  • Yayin da ake shirye-shiryen aikin hajjin bana 2024, hukumar jin daɗin alhazai ta bankaɗo wata matsala da ta kunno kai
  • A wata sanarwa ranar Alhamis, NAHCON ta gargaɗi mahajjata su yi hattara da wasu ƴan damfara da ke neman su ƙara kudi
  • A cewar hukumar, ba ta nemi kowane mahajjaci ya kara wasu kuɗi ba bayan N1.9m, ta faɗi matakin da ya kamata su ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara gargaɗin mahajjatan Najeriya da su yi hattara da wasu ƴan damfara da suka ɓullo.

Wannan gargaɗi na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

Alhazai a gaban Ka'aba.
NAHCON ta gargaɗi alhazan Najeriya Hoto: Inside Haramain
Asali: Twitter

Hukumar ta roƙi maniyyata su kai rahoton duk mutumin da ya nemi su ƙara biyan wasu ƙarin kuɗi bayan kuɗin da aka ƙayyade a hukumance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAHCON ta ja kunnen mahajjata

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, NAHCON ta ja kunnen kowane mahajjaci ya guji biyan ƙarin wasu kuɗi baya ga kuɗin da ya biya na aikin hajjin 2024.

"Hukumar alhazai ta Najeriya tana ƙara yin wani muhimmin gargadi ga maniyyata game da biyan karin kudin aikin Hajji. NAHCON ba ta umarci alhazai su ƙara biyan wasu kuɗaɗe ba bayan wanda ta bayyana.
"Kuma duk wanda ya nemi mahajjata su biya karin kuɗi a madadin mu ya saɓawa doka da aikin hukumar NAHCON, ba mu ba da umarnin ƙara karɓan wasu kuɗi ba.
"Duk wani maniyyaci da wani ya buƙaci ya ƙara kuɗi, ya tura sunan mutumin, wuri da kuma shaidar neman biya ko rasiɗin biyan kudi ga hukumar NAHCON."

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi muhimman nade-nade 5 a gwamnatinsa

- Fatima Sanda Usara.

Hukumar ta bada mafita

NAHCON ta kuma umarci maniyyata su aika bayanan duk wanda ya nemi su kara kuɗi ta hanyar manhajar Whatsapp a lamba kamar haka, 09071800007.

Daga ƙarshe hukumar ta tunatar da maniyyata cewa su duba shafinta na yanar gizo domin karanta duk wata sanarwa kana su guje wa ƴan damfara, Daily Post ta ruwaito.

Tinubu ya tallafawa hajjin 2024

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta tallafawa aikin hajjin bana da N90bn domin ragewa alhazai tsadar kuɗin kujera.

Wata majiya daga hukumar NAHCON ta bayyana cewa wannan tallafin ne ya sa aka nemi alhazai su cika N1.9m amma da sai ƙarin ya wuce haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel