Jerin Kuɗin Aikin Hajji a Najeriya Tun Daga Farkon Mulkin Buhari a 2015 Zuwa 2024

Jerin Kuɗin Aikin Hajji a Najeriya Tun Daga Farkon Mulkin Buhari a 2015 Zuwa 2024

Yayin da hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin kuɗin sauke farali a bana 2024, almaniyyata da dama sun fara cire rai da zuwa kasa mai tsarki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A ranar Asabar da ta gabata, hukumar ta sanar da ƙarin N1.9m a kan kuɗin da maniyyata suka biya a farko watau N4.9m, ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin dala.

Masallaci mai alfarma.
Yadda musulman Najeriya suka biya hajj tun daga hawan Buhari zuwa 2024 Hoto: Inside Haramain
Asali: Twitter

Sai dai binciken Daily Trust ya nuna cewa wannan lamari bai yi wa mutane daɗi ba, yayin da maniyyata suka fara neman a dawo masu da kuɗinsu, a cewarsu ba za su iya cikawa ba.

A wannan shafin, Legit Hausa ta tattaro muku alƙaluman yadda musulman Najeriya suka biya kuɗin hajji tun daga farkon mulkin Buhari 2015 zuwa yau.

Kudin kujerar hajji a shekarun nan

Kara karanta wannan

Abuja: Farashin Dala ya yi babbar faɗuwa lokaci guda a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

2015

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin ana canjin Dala kan N160, NAHCON ta sanar da kuɗin aikin hajji a shekarar 2015 wanda ya kama daga N758,476.59 zuwa N798,476 ga alhazan jihohin Arewa.

Alhazawan Kudancin Najeriya kuma sun biya kuɗi tsakanin N766,556-N905,556 ya danganta da jihar kowane maniyyaci ya fito.

Wannan na kunshe a sanarwar da kakakin hukumar NAHCON ta ƙasa, Alhaji Uba Mana ya fitar.

2016

A wannan shekara ta 2016 alhazan Najeriya daga Arewa sun biya kuɗin hajji mafi ƙaranci N998, 248.92, matsakaicci N1,047,498.92 da kuma mafi yawa N1,145,998.92.

Haka takwarorinsu na Kudancin Najeriya sun biya kuɗin hajji mafi ƙaranci N1,008,197.42, matsakaici N1,057,447.42 da kuma mafi yawa N1, 155,947.42.

2017

Saɓanin shekarun baya, a 2017 NAHCON ta banbanta kuɗin aikin hajji a jihohi 21 da birnin tarayya Abuja, maimakon ƙayyade farashi iri ɗaya a Arewa da Kudu.

Kara karanta wannan

Kano: Ana kukan kara kudin kujerar Hajji, Abba ya ba maniyyata tallafin kusan N2bn

Kudin hajji a shekarar sun kama kamar haka:

Nasarawa - N1, 544,894.16

Neja - 1,525,483.30

Kaduna - N1, 535,503.68

Kano - N1, 537,859.97

Adamawa - N1, 530,101.18

Yobe - N1, 520,101.18

FCT Abuja - N1, 538,218.62

Bauchi - N1, 523,122.41

Filato - N1, 529,036.80

Zamfara - N1, 510,461.65

Sokoto - N1, 524,618.90

Gombe - N1, 516,118.90

Benuwai - N1, 522,118.90

Kebbi - N1, 534,659.85

Taraba - N1, 521,138.21

Osun - N1, 548,153.42

Jami'an tsaro - N1, 538,379.22

Ogun - N1, 561,943.97

Anambra - N1, 511,173.77

Kwara - N1, 501,571.27

Ekiti - N1, 525,191.27

Edo - N1, 551,331.87

Oyo - N1, 584,069.02

2018

Duk da an yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa kuɗin hajji zai kara tsada a 2018 fiye da shekarar da ta gabata 2017, NAHCON ta yi nasarar rage kuɗin

Duk wani maniyyaci a 2018 ya samu ragin kuɗi daga N50,000 zuwa N100,000 idan aka kwatanta da kuɗin da maniyyata a 2017 suka biya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya karbo sabon bashin biliyoyi, Minista ya fadi inda za a jefa kudin

Wannan ba ƙaramar nasara bace da NAHCON ta samu ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

2019

Hukumar NAHCON ta sanar da cewa kowane maniyyaci ya biya N1.5m a matsayin kuɗin aikin hajji a 2019, wanda ya nuna an samu ƙari fiye da 2018.

An samu ƙarin ne saboda tsadar ayyuka a kasar Saudiyya da kuma tashin farashin canjin Naira zuwa dala.

Sai dai daga bisani hukumar ta sake nazari kan farashin, kuma sanar da cewa an samu ragi daga kuɗin hajjin da aka bayyana tun farko.

Alhazan dukkan jihohi da Abuja da Sojoji sun samu ragin N51,170.45 daga kudin da aka sanar tun farko, in ji sanarwar da NAHCON ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

2020

A wannan shekara da aka yi fama annobar cutar Korona, hukumomin ƙasar Saudiya sun hana duk wanda ba ɗan ƙasa ba ya shiga ya yi aikin hajji a 2020.

Wannan doka ce ta hana ƴan Najeriya kimanin 95,000 zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali. Saudiyya ta dakatar da hajji ne a yunkurin daƙile yaɗuwar Covid-19.

Kara karanta wannan

Gidajen mai sun rage farashin fetur saboda matakin da NNPCL ya ɗauka, an samu bayani

Hukumomin Saudiyya sun zaɓi kalilan daga cikin mazauna ƙasar, suka ba su damar yin hajji tare da kiyaye dokokin ba da tazara da sanya takunkumi. Ƙasahen waje ba su samu zuwa ba ciki har da Najeriya.

2021

A karo na biyu a jere, Saudiyya ta hana mahajjata daga Najeriya da sauran kasashe yin aikin Hajjin 2021 saboda cutar korona.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta sanar cewa za ta ba wa mazauna kasar 60,000 da aka yi wa allurar rigafi damar gudanar da aikin hajjin 2021.

2022

Bayan abin da ya faru a shekaru biyu da suka gabata, alhazan Najeriya sun samu damar zuwa aikin hajji a 2022.

Alhazan da suka yi aikin hajjin 2022 daga Kudancin Najeriya sun biya N2,496,815.29, yayin da takwarorinsu na Arewaci suka biya N2, 449, 607.89.

Jihohin Adamawa da Borno kuma sun biya N2, 408, 197.89 saboda kusancinsu da Saudiyya.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Alhazan jihohi 3 sun nemi a dawo masu da kuɗinsu bayan ƙarin N1.9m

2023

Kuɗin aikin Hajji ya ƙara tashi a 2023, yayin da NAHCON ta ƙayyade adadin kuɗin da maniyyata za su biya a wannan shekara.

Alhazan da suka tashi daga Yola da Maiduguri sun biya N2,8000,000 yayin da na sauran jihohin Arewa suka biya N2,919,000.00 kacal.

A cewar NAHCON, Kudancin kasar nan na da nau’ukan farashin hajji guda shida a 2023 wanda ya haɗa da N2,968,000.00 ga maniyyatan Edo, N2,180,000.000 ga alhazan Ekiti.

Alhazan da suka fito daga Kuros Riba sun biya N2,943,000.00, na Osun kuma sun biya N2,983,000.00 yayin da maniyyatan jihohin Legas, Ogun da Oyo suka biya N2,999,000.000.

2024

Tun da farko dai NAHCON ta sanya farashin kudin aikin hajjin bana 2024 a kan N4.9m, to amma saboda karyewar darajar Naira hukumar ta sanar da ƙarin N1.9m

Wannan ƙarin na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Lahadi da ta gabata.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo: Bankin CBN ya karya farashin Dala a Najeriya, ya aike da saƙo ga ƴan canji

Hukumar ta kuma umarci kowane maniyyaci ya cika ragowar kuɗin da aka ƙara daga ranar zuwa 28 ga watan Maris, 2024.

Wannan lamari dai ya sa maniyyata da dama sun fara cire rai da sauke farali a bana, a cewarsu ba su da damar ƙara cika kuɗin da aka nema.

Maniyyatan Kano sun samu rangwame

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyacin aikin hajjin 2024 a jihar.

Gwamna Yusuf ya ce tallafin N500,000 zai shafi wadanda suka biya Naira miliyan 4.9 na farko kuma aka bukaci su biya karin Naira miliyan 1.9.

Asali: Legit.ng

Online view pixel