Kungiyar Kudu Ta Shiga Sabgar Arewa, Ta Ba Gwamna Shawara Kan Matawalle

Kungiyar Kudu Ta Shiga Sabgar Arewa, Ta Ba Gwamna Shawara Kan Matawalle

  • Kungiyar Southern Nigeria Youth Movement ta gargadi gwamnan jihar Zamfara kan matsalar tsaro a jihar
  • Kungiyar ta shawarci Dauda Lawal da ya maida hankali kan dakile matsalar tsaro ba sukar tsohon gwamna, Bello Matawalle ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigimar tsakanin gwamnan da kuma karamin ministan tsaron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Wata kungiya daga Kudancin Najeriya ta shawarci Gwamna Dauda Lawal ya rage yawan sukar tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Kungiyar mai suna Southern Nigeria Youth Movement ta shawarci Dauda Lawal da ya maida hankali wurin tabbatar da dakile matsalar tsaro da ya yi katutu a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Kaduna, Gwamnan APC ya zargi uban gidansa da yashe lalitar gwamnati gaba ɗaya

Kungiya ta ba gwamnan Arewa shawara kan sukar Matawalle da ya ke yi
Kungiya a Kudancin Najeriya ta kare Bello Matawalle inda ta ba Gwamna Dauda Lawal shawara. Hoto: Dauda Lawal Dare, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Ta bayyana yadda Zamfara ke cikin masifa

Ta ce abin takaici ne yadda jihar ke cikin masifa amma kuma gwamnan ya tsaya ga na tsakalar Matawalle kan wasu abubuwa, a cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Kwamred Ikechukwu Okeke shi ya ba da wannan shawara a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ikechukwu ya ce kanana hukumomi 14 a jihar na fuskantar barazanar hare-hare amma gwamnan na ci gaba zargin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.

Wace shawara kungiyar ta ba gwamnan Zamfara?

"A kullum jihar Zamfara na cikin matsifar garkuwa da mutane da ta'addanci da matsalar karbar kudin fansa tare da tarwatsa mutanen garuruwa da dama."
"A yanzu haka, Dauda Lawal ba ya Najeriya yayin da kananan hukumomi 14 ke cikin masifa da hare-haren 'yan bindiga."
"Kungiyar Southern Nigeria Youth Movement ta na tunatar da Dauda Lawal cewa Shugaba Tinubu ya nada Matawalle muƙamin kula da tsaron kasar baki daya."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

- Ikechukwu Okeke

Kungiyar ta ce an nada Matawalle ne domin dakile matsalolin tsaro da suka shafi garkuwa da mutane da ta'addanci da fashi da makami da sauran laifuffuka, Leadership ta tattaro labarin.

APC ta gargadi Dauda Lawal kan Matawalle

Kun ji cewa jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma ta gargadi jami'yyar PDP a jihar Zamfara kan yada sharri ga tsohon gwamna, Bello Matawalle.

Jam'iyyar ta yi martanin ne kan jita-jitar cewa Matawalle ya raba kayan abinci ga 'yan ta'adda a wannan wata na Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel