Yaki da Rashawa: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shugaban PCACC Na Kano, Muhuyi Magaji
- Kotun da'ar ma'aikata ta dauki tsattsauran mataki kan shugaban hukumar PCACC na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado
- An ruwaito cewa kotun ta tsige Rimingado daga mukaminsa, biyo bayan gurfanar da shi da aka yi a gabanta kan zargin karbar cin hanci
- Sai dai wata majiya ta bayyana cewa akwai yiwuwar Rimingado ya daukaka karar hukuncin saboda kotun ba ta hurumin hukunta shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun da'ar ma'aikata (CCT) ta dakatar da shugaban hukumar karbar korafin jama'a da yaki da rashawa (PCACC) na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
Kotun ta dakatar da Rimingado ne biyo bayan zarginsa da ake yi da aikata laifuffuka da suka shafi karbar cin hanci da karya dokar aikin gwamnati.
An gurfanar da shugaban PCACC a kotu
A ranar Alhamis ne jaridar Leadership ta ruwaito cewa an gurfanar da Rimingado a gaban kotun da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tuhumar shugaban hukumar PCACC da boye gaskiya yayin bayyana kadarar da ya mallaka, da kuma karbar cin hanci da rashawa.
Kotun ta yanke hukunci kan cewar ta dakatar da Rimingado daga mukaminsa har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar.
Wata majiya ta shaida cewa akwai yiwuwa za a daukaka karar hukuncin bisa la'akari da cewa akwai dokar kotu da ta haramta a gurfanar da Rimingado.
EFCC, ICPC da CCB na tuhumar Magaji
Jaridar Business Post ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da gwamnatin tarayya gaban babbar kotu kan abin da ta kira cin zarafin shugaban hukumar na PCACC.
Wannan ya biyo bayan wata gayyata da hukumar EFCC, ICPC da kotun CCB suka yi wa Rimingado da nufin yi masa tambayoyi kan yadda aka tafiyar da hukumar daga 2011 zuwa lokacin.
A hukuncin da Mai shari'a Farouk Adamu ya yanke, babbar kotun ta dakatar da hukumomin da kotun tarayyar daga gayyata, tuhuma ko daukar mataki kan ma'aikatan hukumar PCACC.
An haramta fina-finan daba a Kano
A wani labarin daga jihar Kano, hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ta haramta yin fina-finan daba da daudu a Kano.
Abba El-Mustapha wanda ya sanar da wannan matakin a shafinsa na Facebook ya ce an haramta ire-iren fina-finan ne saboda cin karo da dabi'u masu kyau da suka yi.
Asali: Legit.ng