Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado
- Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado
- Lauyan Rimin Gado ya bayyana a gaban majalisar a yau kuma ya sanar da cewa bashi da lafiya
- Sai dai lauyan yace har yau ba a basu wasikar dakatarwa ba, kwafin zargi da ake masa ko korafi
Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, dakataccen shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano.
Kwamitin wucin-gadi na majalisar a wata takarda da suka fitar a farkon makon nan, sun bukaci Rimin Gado da ya bayyana a gaban majalisar da karfe 12 na ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Da duminsa: Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m
Amma kuma a yayin jawabi ga manema labarai bayan bayyanarsa a gaban majalisar, sakataren kwamitin wucin-gadin, Abdullahi A. Bature ya ce zaman ba zai cigaba ba saboda kwamitin sun kafa tsarin bincikar Rimin Gado kamar yadda wasikar lauyansa ta bukata a ranar Laraba.
Bature wanda shine mataimakin daraktan shari'a na majalisar, yayi bayanin cewa Rimin Gado ya ce ba zai iya halartar zaman ba saboda rashin lafiya kuma sun bukaci takardu kuma za a basu.
A zama na gaba, Bature ya ce kwamitin zai yi martani kan wasikar da Rimin Gado ya aiko musu kuma za a mika musu gayyata idan akwai bukatar hakan, Daily Trust ta ruwaito.
Lauyan Rimin Gado, Usman Umar Fari, ya tabbatar da cewa wanda yake karewa bai samu damar zuwa ba saboda bashi da lafiya kuma suna bukatar dukkan abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin bashi kariya.
"An dakatar da Magaji a ranar 5 ga watan Yuli kuma babu wata takarda da aka mika masa ta hakan har yau, ba a bashi takardar dakatarwa ba kuma ba a bashi kwafin zargin da ake masa ba.
"Takardar da muka samu ita ce wasika mai kwanan wata 12 ga Yuli wacce ke gayyatarsa gaban kwamiti ba tare da an saka sunansa ba balle na mai kara ko kuma zargin da ake masa," yace.
A wani labari na daban, a kalla miyagun 'yan bindiga 120 ne suka sheka barzahu sakamakon luguden ruwan wuta da sojojin sama suka yi wa 'yan ta'addan a dajin Sububu dake jihar Zamfara.
An kaddamar da luguden a ranar Litinin bayan wasu mazauna yankin sun sanar da jami'an tsaro sauka da kaiwa da kawowar 'yan bindiga masu tarin yawa a kusa da Sububu.
Wani jami'in sirri ya sanar da PRNigeria cewa an tura jirgin yaki domin dubawa tare da tattaro hotuna da kuma duba yadda 'yan bindigan ke al'amura kafin a kaddamar da harin.
Asali: Legit.ng