'Yan Bindiga Sun Hallaka Farfesa Tare da Sace Mutum 2 a Wani Sabon Hari

'Yan Bindiga Sun Hallaka Farfesa Tare da Sace Mutum 2 a Wani Sabon Hari

  • Ƴan bindiga sun kai wani harin ta'addanci a wani wurin taro da ke Iperu, mahaifar gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun
  • Tsagerun ɗauke da bindigogi cikin baƙaƙen kaya sun hallaka wani Farfesa a jami'ar Babcock bayan ya ƙi yarda su yi garkuwa da shi
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce an cafke wani mutum ɗaya da ake zargi da hannunsa a kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Wasu ƴan bindiga sun kashe wani malamin jami’ar Babcock, Farfesa Illisan Olowojobi Yinka, a wani wurin taro da ke Iperu.

Lamarin ya faru ne a mahaifar Mai girma gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun.

Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutane biyu a yayin harin da suka kai a wurin taron wanda ya firgita mutane da dama.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mazauna kauyen Zamfara sun nemi mafaka a gidan gwamnati

'Yan bindiga sun kai hari a Ogun
'Yan bindiga sun hallaka Farfesa a jihar Ogun Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka kai hari

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan su takwas sun kai farmaki a wurin taro na Ajadeh da ke kan titin Sagamu a yankin Iperu da misalin ƙarfe 9:20 na daren ranar Juma’a da ta gabata.

Maharan, sanye da baƙaƙen kaya sun yi harbi kan mai uwa da wabi kan mutanen da ke shaƙatawa a cikin falon wurin, lamarin da ya sanya mutane suka yi ƙoƙarin tserewa.

An bayyana cewa maharan sun kama malamin jami'ar ne sannan suka harbe shi a ƙirji lokacin da ya ƙi amincewa su tafi da shi.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ta ce an kama wani jami’in tsaro da ya fara aiki a wurin taron makonni biyu kafin faruwar lamarin, cewar rahoton tashar Channels.

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin addinin da 'yan bindiga suka sace ya shaki iskar 'yanci

"Rahoto daga yankin Iperu ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane da kuma kisan kai a ranar 19 ga watan Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 9:20 na dare."
"Shaidun gani da ido sun iya ƙirga wasu mutane takwas sanye da baƙaƙen kaya ɗauke da bindigogi waɗanda suka buɗe wuta a wurin kan mai uwa da wabi."
"An harbi wani mutum ɗaya a ƙirji wanda aka gano malamin jami'ar Babcock ne mai suna Olowojobi Yinka, saboda ya ƙi yarda su tafi da shi."
"An kai shi asibitin koyarwa na jami’ar Babcock, inda aka tabbatar da rasuwarsa. Ana ci gaba da ƙoƙarin kamo masu laifin tare da kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su."

- SP Omolola Odutola

Ƴan bindiga sun hallaka mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum 23 ne suka rasa ransu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki kauyen Anguwan Danko a jihar Kaduna.

Ƙauyen yana kusa da Dogon Dawa a gabashin ƙaramar hukumar Birnin Gwari wacce ke da iyaka da da jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel