Miyagu Sun Kutsa Kai Gidan Dattijo Mai Shekaru 80, Sun Yi Ajalinsa da Matarsa a Arewa

Miyagu Sun Kutsa Kai Gidan Dattijo Mai Shekaru 80, Sun Yi Ajalinsa da Matarsa a Arewa

  • Wasu miyagu sun yi wa mata da miji kisan gilla bayan sun kutsa kai har cikin gidansu tare da yi yanke musu makogwaro
  • Dattijon mai shekaru 80, Adebola Ezekiel da matarsa, Abiodun Ezekiel sun rasa ransu ne a ranar Litinin 1 ga watan Maris
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a birnin, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar mummunan lamarin a yau Laraba 3 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – An shiga tashin hankali bayan wasu miyagu sun hallaka dattijo mai shekaru 80 da matarsa a birnin Abuja.

Dattijon mai suna Adebola Ezekiel da mai dakinsa, Abiodun Ezekiel sun rasa ransu a ranar Litinin1 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC zai ɗauki sababbin ma'aikata sama da 5,000 a jiharsa, ya faɗi dalili

Miyagu sun yi ajalin dattijo mai shekaru 80 da matarsa
An shiga yanayi bayan miyagu sun yi ajalin wani dattijo mai shekaru 80 da matarsa a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Mummunan yanayi da aka tsinci gawawwakinsu

Daily Trust ta tattaro cewa an samu gawarwakin dattawan ne a cikin dakin kwanansu da ke Legislative Quarters a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanayin da aka tsinci gawar dattijon babu dadin gani, yana zaune a kan kujerar guragu yayin da aka yanka masa makogwaro.

Dan cikin marigayin shi ne tuntubi masu gadi a yankin yayin da ya yi ta kiran lambar wayoyin iyayen nasa ba su dauka ba.

Masu gadin sun balla kofar dakin inda suka tsinci gawawwakin dattawan a cikin jini babu kyan gani.

Martanin rundunar 'yan sanda kan lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sanda a birnin Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Laraba 3 ga watan Afrilu.

Adeh ta ce a yanzu haka rundunar ta fara bincike domin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagu sun kutsa kai har ofis, sun kashe babban malamin jami'ar Arewa

“Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Afrilu yayin da wani Seun Ezekiel ya kira jamian ‘yan sanda a yankin.”
“Bayan an fasa dakunan gidan, an samu gawarwakin Adebola Ezekiel da Abiodun Ezekiel a cikin jini an yanke makogwaronsu.”
“Kwamishinan ‘yan sanda a birnin ya ziyarci inda lamarin ya faru inda ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin domin gano bakin zaren.”

- Josephine Adeh

An tsinci gawar lakcara a ofishinsa

A baya, mun kawo muku labarin cewa wasu miyagu sun kutsa kai har cikin ofishin wani lakcara a Jami’ar Maiduguri inda suka yi ajalinsa.

Marigayin Dakta Kamar Abdulkadir ya rasa ransa ne a ranar Lahadi 31 ga watan Maris bayan harin da aka kai masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel