Cross River: Ma’aikatan Gwamnati Sun Fito Zanga-Zaga Kan Wani Dalili 1 Tak, Bidiyo Ya Yadu

Cross River: Ma’aikatan Gwamnati Sun Fito Zanga-Zaga Kan Wani Dalili 1 Tak, Bidiyo Ya Yadu

  • Sabuwar zanga-zaga ta barke a Calabar, babban birnin jihar Cross River, inda ma'aikatan gwamnati ke adawa da rashin biyan su albashi
  • Kamar yadda bidiyon zanga-zagar ya yadu, an ga yadda masu zanga-zagar suka mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar
  • Masu zanga-zagar sun ce har yanzu da watanni Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashi ba, yayin da suke kokawa kan tsadar rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu ma'aikatan gwamnati a jihar Cross River sun fara zanga-zagar nuna bacin rai kan rashin biyan su albashi da har yanzu gwamnatin ba ta yi ba.

Zanga-zagar ta barke ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Valentine: An raba wa ma'aikata kororon roba kyauta a bikin ranar masoya a Osun

Cross River: Ma'aikatan gwamnati sun fito zanga-zaga kan rashin biyansu albashi.
Cross River: Ma'aikatan gwamnati sun fito zanga-zaga kan rashin biyansu albashi. Hoto: Bassy Otu
Asali: Twitter

An nemi masu zanga-zagar su rubuta korafi a hukumance

Ma'aikatan sun yi zuga tare da mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mr. Anthony Owan Enoh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar masu zanga-zagar, yunwa na yunkurin ganin bayan su yayin da har watan Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashi ba.

Sai dai ofishin sakataren gwamnatin jihar ya nemi masu zanga-zagar da su rubuta korafi akan hakan a hukumance.

Bidiyon yadda ma'aikatan suka gudanar da zanga-zangar

Da ya ke wallafa bidiyon yadda zanga-zangar ke gudana, Anthony Ehilebo, wani ma'abocin kafofin watsa labarai ya ce:

"Kai tsaye daga birnin Calabar. Abin da ke faruwa a ofishin sakataren gwamnati kenan. Da alama Najeriya na dab da tarwatsewa. Tattalin arziki ya kara ta'azzara a wannan gwamnati."

Kalli bidiyon yadda zanga-zangar ta gudana:

Fadar shugaban kasa da gwamnonin PDP sun yi musayar yawu

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Tun da fari dai gwamnatin Bola Tinubu ta zargi gwamnoni da kara jefa kasar cikin mawuyacin hali ta hanyar kin biyan ma'aikata albashi.

Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan a matsayin martani na zarginta da zababbun gwamnonin PDP suka yi na cewar tsare-tsaren Tinubu sun jawo yunwa da tsadar rayuwa.

To sai dai kuma jihar Cross River na karkashin gwamnan APC, Bassey Otu, kuma irin hakan take faruwa na a biya wasu a ki biyan wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel