Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai da Yawa a Watan Azumi, Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai da Yawa a Watan Azumi, Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

  • Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai masu tulin yawa a yankin Evwreni da ke titin Gabas maso Yamma a Ughelli ta jihar Delta
  • Rahoto ya nuna cewa ɗaliban na kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta a jihar Kuros Riba lokacin da ƴan bindigan suka tare su
  • Najeriya dai na fama da hare-haren garkuwa da mutane wanda ake ganin yana ɗaya cikin ma fi muni a faɗin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai masu tarin yawa waɗanda har yanzun ba a tantance adadinsu ba a jihar Delta.

Ɗaliban sun faɗa hannun ƴan bindiga ne yayin da suke kan hanya a titin Gabas maso Yamma a yankin karamar hukumar Ughelli ta jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin rashin imani ana azumi, sun yi garkuwa da kananan yara 30 a Arewa

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
An kara sace dalibai masu tulin yawa a jihar Delta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Jumu'a, 29 ga watan Maris, 2024, amma har kawo yanzu babu wasu cikakken bayani kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaliban na cikin mota ƙirar Sienna suna hanyar dawowa ne daga Kalabar, babban birnin jihar Kuros Riba lokacin da maharan suka mamaye su, Channels tv ta ruwaito.

Ƴan bindiga sun aiko da saƙo

Jaridar Vanguard ta rahoto wata majiya daga cikin jami'an tsaro na cewa ƴan bindiga sun kira waya, sun nemi fansar N10m kafin su sako ɗaliban da suka sace.

Har kawo yanzun da muke haɗa wannan rahoton hukumomin tsaro ba su ce komai ba game da sace ɗaliban.

Legit Hausa ta tattaro cewa Najeriya na fama da matsalar garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa wanda ake ganin yana ɗaya daga cikin mafi muni a faɗin duniya.

Kara karanta wannan

DHQ: Sojoji sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigar da suka sace ɗaliban Kuriga

Daga watan Yuli, 2022 zuwa watan Yuni, 2023, an yi garkuwa da mutane aƙalla 3,495 a hare-hare 585 a faɗin ƙasar nan.

An kashe malami a jami'ar UNIMAID

A wani rahoton kuma Wasu tsageru sun shiga har ofis, sun kashe Dakta Kamal Abdulƙadir a jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno.

Rahoto ya nuna cewa makasan sun buga masa guduma a kai tare da caka masa wuƙa, kana daga bisani suka sace motarsa da wasu kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel