Bayanai Sun Fito Kan Yadda Aka Ceto Daliban da Aka Sace a Jihar Kaduna

Bayanai Sun Fito Kan Yadda Aka Ceto Daliban da Aka Sace a Jihar Kaduna

  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta yi magana kan kuɓutar da ɗaliban da ƴan bindiga suka sace a jihar Kaduna
  • A cikin wata sanarwa da DHQ ta fitar ta ce an ceto ɗaliban ne a jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro
  • A cewar sanar ƴan makarantar da aka ceto sun haɗa da mata mutum 76 da maza mutum 61 bayan sun shafe kwanaki a tsare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, ta tabbatar da samun nasarar ceto ɗalibai 137 da aka sace a jihar Kaduna.

Ɗaliban waɗanda aka ceto sun haɗa da mata 76 da maza 61, bayan an sace su a ƙauyen Kuriga na jihar..

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna Uba Sani ya bayyana babbar damuwarsa

DHQ ta bayyana adadin daliban da aka ceto
DHQ ta ce an ceto daliban ne a jihar Kaduna Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Hukumar sojin ta bayyana hakan ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun Manjo Janar Edward Buba, daraktan yaɗa labarai na tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Sojoji, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin gwamnati a faɗin ƙasar nan, sun ceto ɗaliban da aka sace a wani aikin kuɓutar da su da aka gudanar.
"Waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin su ne waɗanda aka sace daga makarantar da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

A ina aka ceto ɗaliban?

Hedikwatar tsaron ta ce an kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su ne a jihar Zamfara.

Sanarwar ta ƙara da cewa an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ƴan banga a jihar.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya sanar da sako ɗaliban.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, sun ceto mutum 4 da suka sace

Bayan sanarwar, gwamnan bai yi ƙarin bayani ba, amma ya godewa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa ƙoƙarin da ya yi wajen ceto ɗaliban.

An sace yaran ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, lokacin da ƴan bindigan suka kai hari a ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Bayan sace yaran, ƴan bindigan sun ɓuƙaci naira biliyan ɗaya a matsayin kudin fansa kafin su bari su shaƙi iskar ƴanci.

Sai dai hukumar sojin ba ta ce komai ba dangane da ko an biya kuɗin fansa kafin a sako yaran.

An yabawa gwamnati

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin ƙauyen Kuringa a jihar Kaduna, Abdulmalik Sani, wanda ya yaba bisa wannan namijin ƙoƙarin da hukumomi suka yi wajen ceto ɗaliban.

Ya yi nuni da cewa ceto ɗaliban abin a yaba ne inda ya yi kiran da gwamnati ta fito ta yi bayani kan gaskiyar hanyar da aka bi wajen ganin yaran sun kuɓuta daga hannun miyagu.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 10 a titin Kaduna zuwa Abuja

Ya yi addu'ar Allah ya kawo ƙarshen wannan annobar ta rashin tsaro da ake fama da ita wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Ƴan sanda sun fattaki ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaɗuna, sun samu nasarar daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane da ƴan bindiga suka yi.

Ƴan sandan sun kuma raunata da dama daga cikin ƴan bindigan bayan sun yi musayar wuta a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel