Hajjin 2024: Gwamna a Arewa Ya Ba Maniyyatan Jiharsa Tallafin Makudan Kudi

Hajjin 2024: Gwamna a Arewa Ya Ba Maniyyatan Jiharsa Tallafin Makudan Kudi

  • Yayin da ake korafi kan karin kudin kujerar aikin hajji, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ba da tallafi mai tsoka
  • Gwamna ya dauki nauyin biyan N1m ga maniyyatan da suka fara biyan kudin kujerar kafin kara kudin da hukumar ta yi
  • Kakakin hukumar alhazai a jihar, Usman Murtala shi ya bayyana haka a yau Litinin 1 ga watan Afrilu a birnin Dutse

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ragewa maniyyata N1m a cikin kudin kujerar hajji.

Gwamnan ya yi hakan ne bayan hukumar alhazai ta kara kudin kowace kujera da N1.9m a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Jigawa da Bauchi, wani Gwamna ya lale N3.34bn domin maniyyatan Hajji

Gwamnan Arewa ya gwangwaje maniyyata da tallafin kudin kujerar hajji
Gwamna Umar Namadi ya ba maniyyata kyautar N1m a Jigawa. Hoto: Umar Namadi.
Asali: Facebook

Wadanda za su ci gajiyar daga maniyyata

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar alhazai jihar, Usman Murtala ya fitar a yau Litinin 1 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murtala ya ce tallafin na maniyyata ne a jihar da suka fara biyan kudin kujerar aikin Hajj, cewar Premium Times.

"Kowane maniyyaci yanzu zai biya N900,000 madadin N.19m da hukumar alhazai ta kara a kwanakin baya."
"Tun farko, hukumar ta ware kujeru 1,518 ga maniyyata a jihar amma 1,260 ne kadai aka fitar wadanda suka kammala biyan kudin."

- Usman Murtala

Usman ya ce wannan tallafi zai shafi wadanda suka fara biyan kudin ne kafin hukumar ta kara kudin kujerar zuwa N1.9m., cewar Daily Trust.

Hirar Legit Hausa da kakakin hukumar

Legit Hausa ta tabbatar da ba da tallafin ta bakin kakakin hukumar alhazai a jihar Jigawa kan tallafin da gwamnan ya ba maniyyata

Kara karanta wannan

Halin kunci: Coci ya tausayawa al'umma, ya bude kasuwa na musamman domin siyar da kaya da araha

Kakakin hukumar a jihar, Murtala Usman Madobi ya tabbatar da ba da tallafin da gwamnan jihar ya ba maniyyata.

"Gaskiya ne mai girma Gwamna Umar Namadi ya tallafawa dukkan alhazan jihar Jigawa da N1m bayan NAHCON ta kara kudin kujera. "
"Mu daman Jigawa ta zama daban, dalili kuwa shi ne a Jigawa ne gwamnan ya ba da tallafin N2.2bn aka sayi kujeru 500, duk da an rufe mu muna da kujeru a kasa. "

- Murtala Madobi

Kaura ya biya rabin kudin kujerar hajj

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tallafawa dukkan alhazan jiharsa.

Gwamna Muhammed ya amince zai biya kaso 50 na karin ga kowane mahajjaci na jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel