Sojoji Sun Kashe Dumbin ’Yan Bindiga a Jihohi 2 Na Arewa, Sun Lalata Sansaninsu
- Sojoji sun samu nasarar kashe akalla 'yan bindiga 11 a samamen da suka kai jihar Zamfara da Katsina da ke Arewacin Najeriya
- Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun yi nasarar tarwatsa sansanin shugaban ƴan bindiga Hassan Yantagwaye a Zamfara
- Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu a farmakin da sojoji ke ci gaba da kai wa dazuzzukan jihohin Arewa maso Yamma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindiga 11 a wani samame da suka kai maboyarsu a jihar Zamfara da Katsina.
Sojoji sun kashe 'yan biniga a Zamfara
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, ta ce sojojin sun kai samame ne a mabuyar shugaban ’yan bindiga Hassan Yantagwaye da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Talabijin na AIT ya rahoto rundunar sojin ta ce an kai farmakin ne a ranar 29 ga watan Maris, inda ta kara da cewa sojojin sun lalata maboyar ‘yan ta’addan.
“Yantagwaye da tawagarsa suna da alhakin yin garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci a wasu sassan arewa maso yammacin Najeriya.
"A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan a wani artabu da suka yi, inda suka kashe 3 daga cikinsu tare da kwato tarin makamai da alburusai."
- A cewar sanarwar.
Sojoji sun farmaki 'yan bindiga a Katsina
A Katsina, sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a Shawu Kuka, Shinda, Tafki, Gidan Surajo, da Citakushi a Kabai, karamar hukumar Faskari, a ranar 30 ga Maris.
A yayin gumurzun, sojojin sun kashe 'yan ta'adda takwas tare da kwato "bindigogi uku, kakin soji da dimbin hatsi na sace".
Rundunar ta ce dakarunta sun kwace kullin wiwi 441 a kauyen Molegede da ke karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.
Asibitin Sokoto ya magantu kan Dogo Gide
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani asibitin kwararru da ke jihar Sokoto ya ce ba shi da hannu a yi wa ƙasurgmin dan bindiga Dogo Gide magani.
Hukumar gudanarwar asibitin sun ce Dogo Gide bai je wajensu a lokacin da sojoji suka harbe shi, kuma ba su taba yi wa wani dan ta'adda magani ba.
Asali: Legit.ng