Rai Bakon Duniya: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Rasu Yana da Shekara 74

Rai Bakon Duniya: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Rasu Yana da Shekara 74

  • An shiga jimami a jihar Kwara sakamakon rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Peter Kisira
  • Rahotanni sun ce, dattijo Peter Kisira ya rasu yana da shekaru 74 a duniya a ranar Asabar 30 ga watan Maris
  • Gwamna AbdulRaman AbdulRazaq ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ya fitar, inda ya yi masa addu'ar mutuwa ta zama hutu a gare shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara- Tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kwara, Peter Kisira, ya yi bankwana da duniya.

Ɗan siyasar ya rasu ne a ranar Asabar 30 ga watan Maris yana da shekara 74 a duniya.

Peter Kisira ya rasu
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya tabbatar da rasuwar Peter Kisira Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya tabbatar da mutuwar Kisira a ranar Asabar, a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Kasurgumin kwamandan ƴan ta'adda da ya fi damun Mutane a jihar Arewa ya miƙa wuya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna AbdulRahman ya yi ta'aziyya

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye, Kisira ya rasu ne a safiyar ranar Asabar.

Ya ce Gwamna AbdulRazaq ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan rasuwar tsohon mataimakin gwamnan, cewar rahoton TVC News.

Gwamnan ya buƙaci iyalan Kisara da mutanen Baruten da su yi haƙuri da wannan babban rashin da suka yi.

Ya yi nuni da cewa za a tuna da irin rawar da ya taka a aikin gwamnati.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya roƙi Allah ya albarkaci iyalan da ya bari.

Sanarwar na cewa:

"Gwamnan jihar Kwara, AbdulRaman AbdulRazaq, ya yi bakin cikin samun rahoton rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dattijo Peter Kisira, da sanyin safiyar yau, Asabar.
"Tsohon mataimakin gwamnan ya rasu yana da shekaru 74 a duniya, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana kan batun taso Ganduje a gaba sai ya yi murabus

Wanene Peter Kisira?

Ya riƙe muƙamin mataimakin tsohon gwamnan jihar daga ranar 29 ga watan Mayun 2011 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Mista Kisira yayi aiki tare da tsohon gwamna Abdulfatah Ahmed tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019.

Tsohon sanata ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shiga jimami bayan rasuwar Sanata Abubakar Danso Sodangi ya na da shekaru 70 da haihuwa.

Marigayin wanda ya wakilci Nasarawa ta Yamma fiye da shekaru 12 ya rasu ne a jiya Lahadi 10 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel