Tallafin Karatu: Gwamnan APC Ya Rabawa Dalibai 9989 ’Yan Ajin Karshe Kyautar N100m
- Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da rabon tallafin karatu na shekarar karatu ta 2023/2024 ga dalibai 9,989 da aka yaye
- An zabo daliban ne daga mutum 27,314 da suka nemi tallafin a fadin kananan hukumomi 16 na jihar da kuma manyan makarantu
- Bugu da kari, gwamnan ya ba da umarnin raba tallafin karatu a zango na 2022/2023 ga daliban shari'a 107 da suka cancanta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ilorin, Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da rabon tallafin karatu na shekarar 2023/2024 ga dalibai kusan 9,989 da za a yaye.
An tantance dalibai 27,314 daga kananan hukumomin jihar 16 da suka halarci manyan makarantu daban-daban a fadin kasar nan domin samun tallafin.
An ba dalibai tallafin N10,000 a Kwara
Hajiya Mansurat Amuda-Kainike, mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta manyan makarantu ce ta jagoranci tantancewar, kamar yadda aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ruwaito kwamishiniyar ilimi ta manyan makarantu Dr. Mary Arinde na cewa:
“Mun fara biyan tallafin N10,000 ga daliban da suka yi nasara a wajen tantancewa kamar yadda mai girma Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya amince.
"An fara biyan kudin ne a ranar Laraba, 27 ga watan Maris, kuma za a ci gaba da biya har sai mun gama rabon. Muna tura kudin kai tsaye zuwa asusun daliban."
Sanarwar ta bayyana cewa an fara raba kyaututtukan tallafin karatu 100,000 na shekarar 2022/2023 kai tsaye ga dalibai 107 da ke karantar shari'a.
Wannan tallafin, wanda gwamnan ya amince da shi, na da nufin farantawa daliban jihar Kwara rai a shekararsu ta karshe a jami’o’in kasar nan.
Kokarin gwamnatin Kwara kan dalibai
Dokta Arinde ta yaba da kokarin gwamnan na tallafa wa dalibai tare da bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun cike fom na bukatar hakan a shafin gwamnatin jihar na yanar gizo.
Sanarwar ta ambaci cewa ba a karbi bukatar da yawa daga masu neman tallafin ba saboda wasu kurakurai da suka yi.
Kura-kuran sun haɗa da tsallake tambayoyi yayin rajista, ba da lambar rijistar karatu ba daidai ba ko lambar banki ta BVN, ko saka bayanan da ba su dace ba ko na karya.
Kano: Abba ya tallafawa maniyya
Idan muka leka jihar Kano kuwa, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf, ya ba kowane maniyyatan jihar tallafin N500,000.
Wannan na zuwa ne bayan da hukumar aikin Hajji ta kasa ta kara N1.9m a kan kowacce kujerar Hajjin bana, lamarin da ya jawo bacin rai daga maniyyata.
Asali: Legit.ng