NUC ta haramta daukar daliban shari’a a Jami’ar NOUN

NUC ta haramta daukar daliban shari’a a Jami’ar NOUN

LABARAN ILMI

Hukumar NUC ta haramta daukar daliban shari’a a Jami’ar NOUN.

– Hukumar NUC tace ta bada dama a karanta ilmin shari’a a wannan Jami’a ta NOUN.

– Sai dai Hukumar CLE ta Najeriya ta bayyana cewa ba a iya karatun ilmin shari’a sai har an shiga aji.

– Saboda haka, Hukumar NUC tace a dakatar da diban dalibai har sai an warware wannan matsala.

Yanzu dai duk mai shirin karantar ilmin shari’a a Jami’ar NOUN sai ya sake nazari, yayi ma kan sa karatun ta natsu. Don kuwa Hukumar Kula da Jam’i’oi na Kasa ta NUC ta hana a cigaba da daukar dalibai masu karatun kwas din shari’a a Jam’iar National Open University of Nigeria (NOUN). DailyPost ta bayyana wannan rahoto, An dai bayyana haka ne a Ranar Alhamis din nan da Farfesa Julius Okojie wanda shine sakataren NUC; Hukumar da ke kula da harkokin jam’i’oin Kasar nan yake wata zantawa da ‘yan Jaridu. Farfesa Okojie ya bayyana daukar wannan mataki har sai an shawo kan rikicin da ake fama da shi da Hukumar CLE ta Najeriya. Hukumar ta CLE dai ta hana daliban da suka karanci ilmin shari’ar daga Jami’ar NOUN zuwa makarantar koyan shariar ta Najeriya (Watau Nigerian Law School), Hukumar tana mai cewa, babu yadda za ayi a koyar da ilmin Shari’a ba tare da an shiga ajin koyarwa an dauki darasi ba.

NUC ta haramta daukar daliban shari’a a Jami’ar NOUN

 

 

 

 

 

 

Hukumar NUC dai tace ana kokarin ganin an shawo kan matsalar; wanda tsakanin su ne da Hukumar CLE da kuma Jami’ar ta NOUN. Matakin da aka dauka dai yanzu shine, za a tsaida daukar sababbin dalibai a Jami’ar (Masu karantar ilmin shari’ar), wannan zai hana samun wata matsalar kan wata. Tabbas, mun amince da karatun ilmin shari’a a wannan Jami’a (Ta NOUN) inji NUC. Wannan ba aikin kowa bane, namu ne, Inji Hukumar NUC mai kula da Jam’i’oin Najeriya.

A wancan watan ne dai Hukumar ta NUC tare da ICPC suka rufe wata Jami’a mai suna World Mission University, da ba ta cika ka’doji ba, a Yankin Delta, aka kuma kama malamai da ma’aikatar makarantara.

KU KARANTA: FASHOLA NA IYA BAKIN KOKARIN SA INJI EL RUFAI

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng