Malabu: EFCC Ta Gaza Gabatar da Hujjoji, Kotu Ta Wanke Adoke Daga Zargin Rashawa
- Wata babbar kotu a Abuja ta wanke tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke, daga laifin zamba a cinikin rijiyar man Malabu
- Kotun a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, ta kuma sallami wasu biyar da ake tuhuma a karar da hukumar EFCC ta shigar
- A cewar alkalin kotun, Mai shari’a Abubakar Kutigi, EFCC ta gaza gabatar da hujjoji na zargin zamba, cin hanci da take yi wa Adoke
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja, FCT - Wata babbar kotu a Abuja ta wanke Mohammed Adoke, tsohon ministan shari'a da wasu mutane shida da ake tuhuma da laifin zamba a cinikin mai na Malabu.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Bello Adoke a gaban kotun bisa zargin ya karbi rashawar N300m, wanda a yanzu aka wanke shi daga dukkan zargi.
Sauran wadanda kotun ta wanke su a ranar Alhamis 28 ga watan Maris su ne Aliyu Abubakar da kamfanonin Malabu Oil and Gas; Nigeria Agip Exploration; Shell Nigeria Extra Deep da Shell Nigeria Exploration Production.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifuffukan da ake tuhumar Adoke
Mai shari’a Abubakar Kutigi ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kasa tabbatar da tuhumar zamba, cin hanci da kuma karkatar da kudade da take yi wa Adoke.
Kutigi ya ce hukumar tattara kudin shiga ta tarayya FIRS ko wata hukuma ba su iya tabbatar da zargin kin biyan harajin da ake yi wa kamfanin Shell da Eni ba.
A kan zargin cin hancin Naira miliyan 300 da aka ce Adoke ya karba, kotun ta ce EFCC ba ta bayar da hujjojin da suka tabbatar da zargin ba, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
Tuhumar da EFCC ke yi wa Adoke
A ranar 15 ga watan Junairu, 2020 ne EFCC ta gurfanar da Adoke a gaban babbar kotun Abuja, bisa zargin karbar Naira miliyan 300 daga hannun Aliyu Abubakar.
An zarge shi da hada baki da sauran wadanda ake tuhuma don "aikata laifi na rashin bin umarnin doka da kuma kare wani daga tuhuma da hana kwace kadarori."
Adoke ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kulla masa sharri a madadin iyalan Abacha da suke tunanin an zalunce a cinikin OPL 245.
"Yadda za a dakile rashawa" - Sanata
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon sanata daga Kaduna, Shehu Sani, ya ce har sai an sake fasalin Najeriya ne za a dakile cin hanci da rashawa.
Sanata Shehu Sani ya nuna cewa akwai jan aiki a gaban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, domin cin hanci da rashawa ya dade yana ci da shuwagabanni tuwo a kwarya.
Asali: Legit.ng