Shehu Sani Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Bi Domin Magance Cin Hanci da rashawa a Najeriya

Shehu Sani Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Bi Domin Magance Cin Hanci da rashawa a Najeriya

  • Sanata Shehu Sani ya ce babu wata hanya da ta fi dacewa a daƙile cin hanci da rashawa a Najeriya kamar a sake fasalin ƙasar nan
  • Sani ya ce sadaukarwar da gwamnatin Bola Tinubu take iƙirarin ta yi bayan cire tallafin man fetur, bai kamata ya zama ɓangare ɗaya ba
  • Tsohon sanatan daga jihar Kaduna yayi magana ne a wata tattauna a shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) wacce Legit.ng ta haɗa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kaduna, jihar Kaduna - Shehu Sani, tsohon Sanata daga Kaduna, ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu da ta ba da fifiko wajen “sake fasalin Najeriya” domin daƙile cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An bankado babban sanata mai daukar nauyin ta'addanci a Arewa

Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kwanan nan akan wata tattaunawa a shafin X wacce Legit.ng ta shirya.

Yadda za a magance cin hanci
Shehu Sani ya fadi yadda za a magance cin hanci da rashawa a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shehu Sani
Asali: Facebook

Sani ya ba da shawarwari kan yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya

Tsohon sanatan ya tabbatar da cewa har yanzu jami’an gwamnati ba su nuna rage kashe kuɗi wajen gudanar da mulki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa lokaci ya yi da ƴan siyasa da masu faɗa aji za su ƙara sadaukarwa wacce za ta amfanar da talakawan ƙasar nan.

A kalamansa:

"Babu wata hanyar da ta fi dacewa ta daƙile cin hanci da rashawa da ta wuce aiwatar da sake fasalin ƙasar nan.
"Inda aka cire tallafin man fetur, mutane suna shan wahala, ba za su iya biyan haya ba, ba za su iya biyan kuɗin makaranta na ƴaƴansu ba, ba za su iya safarar kansu ba, sannan kuma masu rike da madafun iko suna rayuwa mai kyau. Hakan na nufin sadaukarwar ɓangare ɗaya ce.

Kara karanta wannan

Sanata ya fallasa yadda wasu 'Hadimai' suka talauta dukiyar Najeriya a mulkin Buhari kafin 2023

"Don haka, ina ganin rage kuɗin gudanar da mulki shi ne farko. Na biyu kuma, sadaukarwa ya kamata ta kasance a kowane ɓangare. Ba zai yiwu a ƙara kuɗin karatu ga yaran talakawa a makarantun gwamnati ba. Akwai kuɗin da za a samar da ilimi ga ƴaƴan talakawa."

Shehu Sani Ya Yabi Gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shehu Sani ya yabi gwamnatin Shugaba Tinubu kan fannin tsaro.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel