Yanzu Yanzu: Zargin rashawa: Tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke ya isa kotu don gurfanar dashi
- Tsohon Atoni Janar na tarayya, Mohammed Adoke ya isa babbar kotun tarayya da ke Gwagwalada, Abuja, domin gurfanar dashi kan badakala kudi
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ke tuhumarsa da damfarar kudi dala biliyan 1.09 na man Malabu
- Sauran da ke fuskantar shari’a tare dashi sune; Nigeria Agip Exploration Limited(ENI); Shell Nigeria Ultra Deep Limited; Shell Nigeria Exploration Production Company Limited; Malabu Oil and Gas Limited; Aliyu Abubakar da kuma Rasky Gbinigie
Tsohon Atoni Janar na tarayya, Mohammed Adoke ya isa babbar kotun tarayya da ke Gwagwalada, Abuja, domin gurfanar dashi kan tuhume-tuhumen damfara da sauran su da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke yi masa.
An kawo shi kotu cikin wata motar bas cike da jami’an EFCC da wasu yan sanda.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a ranar Litinin ta sany tuhume-tuhume 42 kan tsohon Atoni Janar din tarayya Lima tsohon ministan shari’a, Mista Mohammed Bello Adoke (SAN), da wasu mutane shida da ke da nasaba da badakalar dala biliyan 1.09 na man Malabu.
KU KARANTA KUMA: Gwamnonin arewa sun nuna bakin ciki kan kisan babban faston Adamawa
Sauran da ke fuskantar shari’a sune; Nigeria Agip Exploration Limited(ENI); Shell Nigeria Ultra Deep Limited; Shell Nigeria Exploration Production Company Limited; Malabu Oil and Gas Limited; Aliyu Abubakar da kuma Rasky Gbinigie.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng